
Bayan dirkawa budurwarsa ciki ta haihu, ya kasheta da duka a kan kudin ciyarwa
Tuesday, 8 December 2020
Comment

Wani David mai shekaru 27 ya daki karuwarsa, wacce ta haifa masa diya mace har ta kai ga mutuwa Kamar yadda makwabta suka tabbatar, sun ji ihunta da misalin 11:30 na dare, yayin da yake bugunta
Al'amarin ya faru a jihar Bayelsa a ranar Lahadi da daddare, inda ya rufe kofa ya cigaba da kirbarta Wani Promise David mai shekaru 27 yayi wa karuwarsa, Esther Pascal, mai shekaru 18 dukan kawo wuka har ta kai ga mutuwa sakamakon fada a kan abinci da kudin kulawa da diyarsa.
Al'amarin ya faru ne a ranar Lahadi da tsakar dare a layin Ebis Machanic, Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa. Marigayiyar ta haifa wa mutumin mai aiki a wani wurin wanke mota, yarinya wacce yanzu shekarunta 2 da haihuwa, The Nation ta wallafa.
Wasu makwabtansu sun ce fadan tsakanin masoyan ya dade yana faruwa. Sun ce sun farka da misalin 11:30pm na ranar Lahadi, sakamakon jin ihun matar tana neman taimako. A cewar shaidar: "Lokacin da muka isa bakin kofar, sai muka fahimci an kulle kofar ta cikin dakin.
Sai da muka balla kofar tukunna muka ga matar a kasa. "Mun yi kokarin debo ruwa don mu yayyafa mata, ashe ba suma tayi ba, mutuwa tayi. Take a nan muka kira 'yan sanda muka sanar da su da abinda ya faru."
Wasu daga cikin ganau din, sun ce mutumin ya buga mata wani abu mai nauyi a kanta, wasu kuma suka ce naushinta yayi a kai. Yanzu haka wasu 'yan kungiyar GRI wacce matar gwamnan Bayelsa ta kirkira, Mrs. Gloria Diri, sun je wurin da abin ya faru.
Dise Sheila Ogbise, wata lauya, wacce ita ce mataimakiyar shugaban GRI ta ce al'amarin ya kazanta, kuma ta yi kira a kan bukatar yadda za a kawo karshen zaluncin mata a gidajensu. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa, Asinim Butswat, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce yanzu haka wanda ake zargin yana hannun 'yan sanda a ofishinsu dake Ekeki ana cigaba da bincike.
SOURCE: LEGIT
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Bayan dirkawa budurwarsa ciki ta haihu, ya kasheta da duka a kan kudin ciyarwa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?