--
Batanci ga Annabi: Kotu ta bada umurnin sakin Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya

Batanci ga Annabi: Kotu ta bada umurnin sakin Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya



Kotu ta bada umurnin sakin, Mubarak Bala, mutumin da ake zargi da yi wa Annabi Muhammad batanci a Facebook


Yan sanda sun kama Mubarak Bala ne tun a watan Fabrairun 2020 a Kaduna daga bisani aka kai shi Kano inda aka cigaba da tsare shi 



Kotun ta yanke cewa an keta hakokinsa na dan adam saboda tsare shi tsawon lokaci ba tare da bashi damar ganin lauyoyinsa ba kuma ta umurci a biya shi N250,000 Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bada umurnin sakin Mubarak Bala, 


wanda ya yi amfanin da shafinsa na Facebook ya wallafa wasu rubutu da ake ganin batanci ne ga Annabi Muhammad (SAW), Daily Trust ta ruwaito. 


An kama, Bala, shugaban Humanist Association of Nigeria, a watan Fabrairu a gidansa da ke Kaduna bayan wasu lauyoyi sun shigar da kara a kansa inda suke zargin ya yi wa Annabi Muhammad batanci a shafinsa na Facebook. 


Yan sandan jihar Kaduna suka kama shi sannan daga bisani aka mayar da shi hannun yan sandan jihar Kano a ranar 2 ga watan Mayun 2020. 


Da ya ke yanke hukunci kan korar da lauyoyin Bala suka shigar na zargin keta hakkinsa na bil adama, Mai shari'a Inyang Ekwo ya ce tsare Bala da 'yan sanda suka yi na tsawon watanni ya keta hakkinsa na 'yanci, adalci, zirga-zirga da 'yancin tofa albarkacin bakinsa. 


"Rashin barin wanda ake zargi ya gana da lauyoyinsa keta hakkinsa na adalcin shari'a ne da samun lauya kamar yadda ya ke a karkashin sashi na 34 da 35(2) a karkashin kudin tsarin kasa ta 1999." 


Alkalin ya kuma umurci rundunar 'yan sanda su biya naira 250,000 ga wanda ake yin karar. Mubarak Bala ya dade yana sukar addini tun bayan ridda daga addinin musulunci a shekarar 2014. 


An kuma gano cewar iyayensa sun taba kai shi zuwa asibitin kwakwalwa a kan tilas a Kano amma daga bisani aka sako shi kuma tun lokacin ya cigaba da samun barazanar kisa. 


Source: Legit 


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Batanci ga Annabi: Kotu ta bada umurnin sakin Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?