--
Batagari sun harbi DPO Yahaya Pawa yayin da ya jagoranci samamen kamen ma su laifi

Batagari sun harbi DPO Yahaya Pawa yayin da ya jagoranci samamen kamen ma su laifi


DPO na ofishin rundunar 'yan sanda da ke Otukpo a Makurdi, SP Yahaya Pawa, ya tsallake rijiya da baya - Wasu batagarin 'yan ta'adda sun dirkawa SP Pawa dalma a yayin da ya jagoranci tawagar 'yan sanda zuwa kamen ma su laifi 


SP Pawa da jami'an tawagarsa sun yi dirar mikiya a kan batagarin a daidai lokacin da su ka baje kolin kayan da suka sato Wasu ɓatagari sun harbi DPO ofishin ƴan sanda da ke Otukpo, SP Yahaya Pawa da safiyar ranar Talata a unguwar Otukpo da ke Makurdi, babban birnin jihar Benue. 


Jaridar Daily Trust ta gano cewa DPO Pawa ya jagoranci tawagar jami'an ƴan sandan don su ƙwamuso wasu masu laifi da ake zargin sun fake a yankin da lamarin ya afku. 


An gano cewa masu laifin suna da hannu dumu dumu a satar kayayyakin da akayi a kasuwar Otukpo lokacin da gobara ta tashi a makon dsa ya gabata. Su na tsakiyar cin kasuwar kayan satar ne, sai tawagar ƴansanda a ƙarƙashin DPO Pawa suka bayyana a wurin da suke kasuwancin. 


Ɓatagarin dai sun yi bajakolin kayayyakin da suka sato daga kantinan ƴan kasuwa, wanda suka haɗar da kayan sawa da sauran kayan amfanin gida, a wajen garin Otukpo kamar yadda labari ya samu rundunar ƴan sanda. 


Ƴan sanda na tsaka da cafke masu laifin sai wasu daga cikinsu suka ɗirkawa DPO alburushi, sannan suka cika bujensu da iska. Da aka tuntuɓe ta, Kakakin rundunar ƴansandan jihar Benue, Catherine Anene, ta tabbatar wa da ƴan jarida faruwar lamarin a Makurdi. 


Anene ta ce"Da gaske ne wasu ɓatagari sun harbi DPO lokacin da ya jagoranci tawagarsa Atisaye." "Amma DPO yana nan da ransa cikin ƙoshin lafiya, sun harbe shi ne a kafaɗa." 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

Related Posts

0 Response to "Batagari sun harbi DPO Yahaya Pawa yayin da ya jagoranci samamen kamen ma su laifi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?