
Barawon da ya kwace motoci 18 a cikin kwanaki 90 ya shiga hannun 'yan sanda
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta damke wani mutum da ya kware wurin satar motoci ta hanyar saka wa mutane bindiga. An gano barawon da ake kira da gwamnati ya yi fashin motoci 18 a cikin kwanaki 90 kacal.
Kamar yadda rundunar ta bayyana, sunan matashin Abdullahi Muhammed amma an fi sanin shi da Gwamnati. Ya kware a fashi da bindiga amma na motoci a cikin jihohin Jos da Bauchi kafin ya shiga hannun rundunar. Rundunar 'yan sandan ta wallafa hotonsa a shafinta na Twitter bayan ta cafke shi.
Abdullahi Mohammed a.k.a ‘Gwamnati’, a specialist in car snatching, snatched, within 90 days, 18 vehicles at gun-point from their owners in Jos and Bauchi States. pic.twitter.com/Yqtet3Kgad
— Nigeria Police Force (@PoliceNG) December 1, 2020
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Barawon da ya kwace motoci 18 a cikin kwanaki 90 ya shiga hannun 'yan sanda "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?