--
Bamu tuntubi kowa ba; Boko Haram ta dauki nauyin sace daliban Kankara a Katsina

Bamu tuntubi kowa ba; Boko Haram ta dauki nauyin sace daliban Kankara a Katsina

Kungiyar Boko Haram ta sanar da daukan alhakin kai hari makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara A ranar Litinin ne gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da cewa wadanda suka sace daliban sun tuntubi gwamnati 


Sai dai, a cikin sakon sautin murya da Shekau ya fitar, ya ce basu tuntubi kowa ba dangane da batun sace daliban Kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ta sanar da cewa ita ce keda alhakin sace dalibai fiye da 300 daga makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara a jihar Katsina, kamar yadda HumAngle ta rawaito. 


A cewar HumAngle, shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya ce har yanzu basu tuntubi kowa dangane da wasu sharuda na sakin daliban ba. Jaridar ta ce, Shekau ya sanar da hakan ne a cikin wani sakon sautin murya mai tsawon mintuna 4:28 da ya fitar da duku-dukun safiyar ranar Talata. 


"Abinda ya faru da Katsina ya faru ne domin daukaka addinin Islama da kuma nuna kyamar karatun Boko wanda ilimi ne na turawan yamma da ya saba da koyarwar Allah da manzonsa. 


"Ba'a koyarwa bisa tsarin Allah da manzonsa a makarantar Boko. Suna rusa addinin Islama. Su na yin hakan ne a sakaye, amma Allah masanin komai ne hatta abinda aka boye. Allah ya daukaka addinin Islama. Allah ya kashemu a matsayin Musulmai," kamar yadda HumAngle ta rawaito cewa Shekau ya fada a cikin sakonsa. 


Sannan ya cigaba da cewa, "a takaice, mu ne keda alhakin abinda ya faru a Katsina," ya fada kafin ya gimtse sakon ta hanyar sanar da cewa shine Shekau, shugaban kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal Jihad. 



Wannan shine karo na farko da kungiyar Boko Haram ta taba fitowa ta sanar da daukan alhakin kai gagarumin harin sace dalibai a jihohin yankin arewa maso yamma. A ranar Litinin ne Jridar Legit.ng ta rawaito cewa Masari ya sanar da shugaba Buhari cewa 'yan bindiga sun tuntubi gwamnatin jiha bayan sun yi awon gaba da daliban makarantar sakandiren Kankara, kamar yadda Channels ta rawaito. 


"Gwamnan, wanda ya samu rakiyar mataimakinsa, Manir Yakubu, ya ce 'yan bindigar sun kira kuma tuni an fara tattaunawa dasu a kan kiyaye lafiyarsu da kuma dawo da su gidajensu cikin koshin lafiya," kamar yadda Garba Shehu ya sanar a cikin jawabin da ya fitar. 


Ya bayyana cewa jami'an tsaro sun hango wurin da daliban suke tare da bayyana cewa ''akwai alamun samun nasara'' dangane da tattaunawar da aka fara. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Bamu tuntubi kowa ba; Boko Haram ta dauki nauyin sace daliban Kankara a Katsina "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?