--
banner
Babu Wani Dan Nijeriyar Da Zai Tsallake Allurar Rigakafin Korona, in ji Lawan

Babu Wani Dan Nijeriyar Da Zai Tsallake Allurar Rigakafin Korona, in ji Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa babu wani dan kasar da za a sauya shi wajen rarrabawa da kuma yin allurar rigakafin cutar korona a lokacin da rigakafin ya iso kasar.



Tuni bangaren zartarwa na gwamnati ta gabatar da kudirin Naira biliyan 400 a gaban Majalisar dokoki ta kasa da nufin sayen alluran rigakafin da za a yi kyauta ga ‘yan Nijeriya.


Lawan, a cikin sakonsa na Kirsimeti a ranar Alhamis, ya ce, “Majalisar dokoki ta kasa tare da tuntubar hukumomin da abin ya shafa za su tabbatar da kwazo wajen sayowa da rarraba maganin rigakafin korona lokacin da ya samu.”


Ya ce, “Wannan zai tabbatar da cewa dukkan ‘yan Najeriya sun samu damar yin allurar rigakafin kwayar cutar mai taurin kai.”


Lawan, da abokan aikin sa a dakin taro na sama, a cikin bayanan su daban, sun kuma bukaci ‘yan Nijeriya, musamman Kiristoci da su kiyaye ka’idojin kariya daga cutar yayin da suke murnar haihuwar Yesu.


Sanatocin a sakonninsu daban-daban, sun bukaci ‘yan Nijeriya da su jure halin da ake ciki domin annobar za ta zama tarihi.


Lawan, a cikin wata sanarwa daga mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Ola Awoniyi, ya bayyana cewa, bikin na bana ya zo ne a daidai lokacin da duniya ke yakar sake barkewar cutar korona.


Ya ce, annobar ta tilastawa kasashe da dama samar da ka’idoji na kare lafiya a daidai lokacin da al’ada mutane ke taruwa don raba soyayya a bikin haihuwar Yesu.


Lawan, duk da haka, ya nuna kwarin gwiwarsa cewa juriya da halaye masu kyau na ‘yan Nijeriya ba zai taimaka wa kasar nan kawai ba wajen shawo kan kalubalen. Ya ce, bin ka’idojin da ba na magunguna ba zai tabbatar da cewa matsalolinsu ba za su dakatar da bikin murnar Kirsimeti a cikin kasar ba.


Ya kara da cewa, “Ina yin biki tare da Kiristoci masu aminci kuma ina umartar mu duka da mu tuna da mahimmancin Bikin. Ganin yadda lamarin ya faru a karo na biyu na yaduwar kwayar cutar, ya kamata mu kiyaye kuma mu cika ka’idojin da ba na magunguna ba da hukumomi suka sanya.”


Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kudi, Solomon Adeola, ya yi kira ga dukkan Kiristoci musamman da kuma ‘yan Nijeriya baki daya da su yi amfani da lokacin Kirsimeti don sabunta imaninsu ga Yesu kuma su bi dukkan matakan taka-tsantsan game da yaduwar cutar korona a duniya.


Sanatan ya yi kira da ayi taka tsan-tsan wajen nuna irin wannan kyakkyawar halayyar ta la’akari da matakan kariya da aka tsara don hanawa da yakar yaduwar cutar a karo na biyu. Ya kuma sanar da sokewarsa karshen shekara shekara ‘yuletide’ wacce galibi ke jan hankalin masu jefa kuri’a da masu fatan alheri na wannan shekarar.


Sanata mai wakiltar gundumar yamma ta yamma, Tolu Odebiyi, a cewar wata sanarwa daga ofishin yada labaran sa, ya isa ga shugabannin da masu kula a duk sassan siyasa a Ogun ta yamma tare da kyautar kyaututtuka. Sanarwar ta bayyana cewa, kyautar karamci ne don karfafa tasirin faduwar tattalin arziki a wannan lokacin bikin.


Wani tsohon gwamnan jihar Enugu kuma Sanata mai wakiltar gundumar Enugu ta Gabas, Dakta Chimaroke Nnamani, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan lokaci na sabuwar shekarar don yin addu’a don hadin kai, zaman lafiya da tsaron Nijeriya.


Nnamani ya bayyana cewa, yanayin rashin tsaro, kashe-kashe, satar mutane, fashi da makami, da sauran muggan laifuka da yanzu suka zama ruwan dare, ya kamata ayi duk mai yuwuwa don dakile wannan yanayi. Ya kuma yarda da kokarin da jami’an tsaro ke yi na dakile matsalar, amma ya nuna damuwarsa cewa kokarin bai samar da sakamakon da ake fata tsammani ba.


Ya ce, “Dole ne a sami sabbin hanyoyin fuskantar kalubalen tsaro ciki har da hadin kai da tura fasahar zamani ta dacewa.”


Har ila yau, wani tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dabid Mark, ya tunatar da ’yan Nijeriya game da tsarkakar kasancewa masu kiyaye ’yan uwansu duk da matsalolin zamantakewar tattalin arziki da tsaro. Don wannan, ya nemi hakuri tsakanin addinai da tsakanin masu aminci ta hanyar da ke ba kowane dan ‘yanci dama. Ya kuma shawarci shuwagabannin addinai da ke fadin kasar nan da su yi wa’azin sakon zaman lafiya, hadin kai da kyakkyawar makwabtaka domin mayar da asarmu Nijeriya matattarar zaman lafiya.


Akan kalubalen tsaro, ya bukaci ‘yan kasa musamman malamai da sarakunan gargajiya da su haa kai da hukumomin tsaro domin kawar da matsalar kasar.


Tsohon mataimakin Mark, Ike Ekweremadu, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi koyi da halayen kauna, wanda ya bayyana a matsayin babban jigon da sakon Kirsimeti.


Ekweremadu, a cewar wata sanarwa daga ofishin yada labaran sa, ya kuma gabatar da kyaututtuka da tallafi ga zawarawa 300 da aka zabo daga gundumar sa ta sanata, a matsayin wani bangare na ayyukan murnar zuwan lokaci.


Ya ce, “A lokacin bikin Kirsimeti, kada mu manta da mahimmancin kyauta da raba kauna”


Source: LEADERSHIP HAUSA

Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app7576

0 Response to "Babu Wani Dan Nijeriyar Da Zai Tsallake Allurar Rigakafin Korona, in ji Lawan"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?