--
Ba zan saka kaya kamar 'yar kauye ba saboda ina da aure, Matar aure ga kotu

Ba zan saka kaya kamar 'yar kauye ba saboda ina da aure, Matar aure ga kotu


Wani Sheriff ya zargi matarsa Rashidat da yin lalata da wani dan sanda, don haka ya bukaci kotu ta raba aurensu 


A cewarsa, tana yin shiga kamar ba matar aure ba, kuma tana lalata da wani dan sanda duk da Rashidat ta musa 


Ta ce ya mayar da ita tamkar jaka, sannan ya sadu da ita ta karfi da yaji, har idonta na hagu ya makantar mata Rashidat, matar Sheriff Ahmed, mai shekaru 44, ta zargi mijinta da takura mata a kan yadda take shiga. 


Ahmed ya maka matarsa a kotu, inda yake bukatar su rabu sakamakon rashin kamun kanta da kuma mummunar shiga. 


Ya kai korafin a wata kotu da ke Igando ranar Litinin, inda ya zargeta da lalata da wani dan sanda, The Cable ta wallafa. 


A cewarsa, ya so ya fatattaki matarsa, amma yadda 'yan uwa da abokan arziki suka sanya baki yasa ya hakura. Kamar yadda NAN ta ruwaito, "Matata bata da kamun kai, har lalata take yi da wani dan sanda. 


"Da na duba wayarta, na ga yadda take kalaman iskanci da soyayya da wannan dan sandan ta kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp. 


"Har fada muka yi akan hakan, na so in fatattaketa amma saboda 'yan uwa da abokan arziki sun sanya baki, na yafe mata.


 "Tana sanya sutturu wadanda basu dace da matar aure ba. Na roke ta a kan ta canja shigarta, da rayuwarta, amma ta ki." Ahmed ya zargi matarsa da yawo da layu a jakarta, sannan tana fita a duk lokacin da ta ga dama. 


Ya bukaci kotu ta raba su don yanzu ta fita daga ransa. Rashidat tace wa kotu ta amince da a kashe aurenta, don ta gaji. Matar mai yara 2 ta musanta yin lalata da dansanda, inda tace kishin mijinta ya yi yawa. 


Ta zargi Sheriff da ci mata mutunci da kuma saduwa da ita ta karfi da yaji. "Ya mayar da ni kamar jakarsa, sannan ya sadu dani ta karfi da yaji bayan ya gama dukana," a cewarta. 


Sai da ya zubar min da ciki sau 2, saboda duka. Sakamakon duka, har idona na hagu na rasa, duk da an yi min aiki, amma har yanzu ba na gani." 


Ta ce ya sha dukanta kamar zai kasheta ana tafiya da ita asibiti, shiyasa ta gudu saboda zai iya kasheta watarana. Alkalin ya raba auren Sheriff da Rashidat, sannan ya bai wa Rashidat damar rike yaran. 


Sheriff zai dinga ba ta N10,000 duk wata kuma ragamar karatu da walwalar yaran tana wuyansa. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Ba zan saka kaya kamar 'yar kauye ba saboda ina da aure, Matar aure ga kotu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?