Ba za a yi zabe ba a 2023, Jigon arewa Yusuf ya kaddamar
Wani babban jigo a arewa, Usman Yusuf, ya fada ma yan siyasan Najeriya da su manta da zaben 2023 - Yusuf ya bayyana cewa matakin rashin tsaro a kasar shine babban abun damuwa a wajen dukkan yan Najeriya
Jigon na arewa ya bayyana cewa babu zaben da za a iya yi a yanayi na hargitsi da rashin kwanciyar hankali Farfesa Usman Yusuf, wani shahararren jigon arewa, ya yi hasashe game da zaben Najeriya na gaba.
A wata hira da jaridar The Sun, Yusuf, wanda ya kasance tsohon sakatare na hukumar inshoran lafiya ta kasa (NHIS), ya ce yan siyasan da ke shirye-shirye don zaben 2023 suna rayuwa ne na muradin karya. Legit.ng ta tattaro cewa jigon na arewa ya jadadda cewa zaben 2023 ba zai taba yiwuwa ba, musamman a arewa, duba ga matakin rashin tsaro a kasar.
Ya bayyana cewa maimakon mayar da hankali wajen kawo karshen ta’addanci a Najeriya, yan siyasa na ta magana game da yankin da Shugaban kasa zai fito a 2023. Yusuf ya ce: “Akwai rashin tsaro a fadin kasar sannan abunda yan siyasa wadanda ke da son kansu ke tattaunawa a koda yaushe- shine garambawul, Shugaban kasar 2023, yankin da Shugaban kasa zai fito.
Muna a 2020, shekara ta farko a zangon shekaru hudu. “A lokacin da Najeriya ke fuskantar rashin tsaro mafi muni a rayuwarta tun yakin basa; a daidai lokacin da asusun jiha ke rawa, a daidai lokacin da mutanenmu ke fuskantar talauci mafi muni da yunwa, yan siyasanmu suna tunanin wa za a mika wa mulki a 2023, maimakon yadda za su fitar damu daga rami, kuma ina mamaki.
“Idan wannan rashin tsaron ya ci gaba a wajajen 2023, ba lallai ne a samu kasa da za a sauya fasalinta ba, ba lallai ne a samu shugabanci da za a mika ba kuma 2023 na iya zama mafarki kawai. Yana iya zama gada da za a dade ba a kai ba."
Source: Legit
0 Response to "Ba za a yi zabe ba a 2023, Jigon arewa Yusuf ya kaddamar "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?