Auren mai mata ya fi komai dadi, yana zuwa da garabasa, In ji matashiya yar Nigeria
Wata matashiya yar Najeriya ta haifar da zazzafan muhawara a shafin Twitter bayan ta bayar da wani shawara a kan auren mai mata
@IlhamSafiyyat ta ce auren mai mata shine zabi mafi kyau da budurwa za ta iya yi - A cewar matashiya, daga cikin tarin alkhairan da ke tattare da hakan shine samun yar’uwa Wata yar Najeriya mai amfani da shafin Twitter @IlhamSafiyyat ta bayyana cewa auren namiji mai mata shine zabi mafi kyau saboda abubuwa da dama da ke tattare da hakan.
@IlhamSaffiyat ta bayyana cewa irin wannan aure na zuwa da garabasa; ga miji sannan ga yar’uwa. Yar’uwa da take nufi a nan shine matar da sabuwar amaryar za ta je ta tarar a gidan mijin.
Mutane da dama sun yi martani a wallafar da matashiyar tayi yayinda suka bayar da nasu ra’ayin kan yadda aure ya kamata ya kasance da kuma irin mutumin da mace za ta zaba.
Yayinda wasu suka caccaketa akai, wasu yan tsiraru sun yarda da shawararta.
Kalli wallafarta a kasa:
Getting married to a married man is the best thing because it comes with a bonus a husband and a sister❤️
— MAR'ATUSSALIHA🧕🌹❤️ (@IlhamSafiyyat) December 13, 2020
Jaridar Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:
@Sir_Babex ya ce: "Allah ya yi maki albarka a kan wannan fahimta taki. Ki ji ma, idan Allah ya yarda sai kin auri mai mata uku, domin ki samu tarin garabasa.”
@khalidGabary ya ce: "Kawai ki fada mana cewa da mai aure kike soyayya.”
@Obasteve91 ya ce: "Ba a kasar Yarbawa ba. Za ki shirya wa kanki da yaranki da basu ji ba basu gani ba gadar kiyayya.”
@Nasir1on1 ya ce: "Bugu da kari za ki zama mata ta lokaci zuwa lokaci: Kwana biyu da miji sannan kwana biyu babu miji. Wani dadi ke cikin haka!”
@KabiruIyayi ya ce: "Kin yi gaskiya, ci gaba biyu kenan.”
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Auren mai mata ya fi komai dadi, yana zuwa da garabasa, In ji matashiya yar Nigeria "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?