--
APC: Mun binciko gwamnan Arewa da ke daukar nauyin ta'addanci a yankin

APC: Mun binciko gwamnan Arewa da ke daukar nauyin ta'addanci a yankin

 
Jam'iyyar APC ta yi ikirarin cewa tana da rahoton binciken sirri da ke nuna wani gwamnan jihar Arewa maso yamma na daukan nauyin 'yan bindiga 

Wannan zargin ya fito ne daga bakin mataimakin kakakin jam'iyyar APC na kasa, Mista Yekini Nabena 


Nabena ya yi kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa su duba rahoton nasu don tabbatar da sahihancinsa da kuma daukan mataki Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki a ƙasa ta zargi wani gwamna mai ci a yanzu da ɗaukan nauyin ƴan bindiga kamar yadda Premium Times ta ruwaito. 


Duk da cewa bata ambaci sunansa ba, jam'iyyar APCn cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis ta yi ikirarin cewa 'binciken sirrin' da ta yi ya nuna cewa wani gwamna daga Arewa maso Yamma yana hada kai da ɓata gari don tada fitina a yankin. 


Wannan zargin na zuwa ne bayan sace yan makarantar sakandare da wasu da ake zargin yan ta'addan kungiyar Boko Haram ne suka yi. 


Duk da maƙuden kuɗaɗen da ake kashewa a kan tsaro, har yanzu gwamnatin tarayya ta gaza kawo karshen hare-haren yan bindiga. Arewa maso yamma yanki ne cikin yankuna shida na Najeriya da ke da jihohi bakwai. 

Jihohin su ne Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara. Jami'yar APC ke mulki a biyar daga cikinsu yayin da PDP ke mulkin jihohi biyu. Da ta ke ƙorafi game da taɓarɓarwar harkar tsaro a kasar, APC ta yi kira ga hukumomin tsaron kasar su dauki matakin gaggawa.


"Rahotonnin binciken sirri da muka yi ya danganta ɗaya daga cikin gwamnonin arewa maso yamma da haɗa kai da ɗaukan nauyin barnar da hare-hare da ƴan bindiga ke yi a yankin. Ba zan bada cikakken bayani ba saboda batun sirri ne wannan. 


"Don haka, muna kira ga hukumomin tsaro da abin ya rataya a kansu suyi bincike bai tabbatar da sahihancinsa. Ran ɗan adam ba abin wasa bane ko abinda za a siyasantar da shi," a cewar mataimakin kakakin APC na kasa, Yekini Nabena. 


Source: Legit 


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "APC: Mun binciko gwamnan Arewa da ke daukar nauyin ta'addanci a yankin"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?