Ango ya dakatar da daurin aure bayan amarya ta yi katobara a 'Facebook'
Tuesday, 22 December 2020
Comment
Wata amarya ta ga 'ta leko, ta koma' bayan angonta ya dakatar da daurin aurensu da za'a yi a cikin watan nan
Amaryar ta yi katobara wajen bayar da amsar cewa 'Eh' za ta iya cin amanar mijinta akan miliyan N1 Rahotanni sun bayyana yadda wani mutum dake dab da angwancewa da budurwarsa ya fasa aurenta sakamakon wani furuci da ta yi karkashin wani rubutu a kafar sada zumunta ta Facebook.
Matar dai ta je ƙarƙashin wani rubutu ne inda wani mutum ya jefa tambaya da cewa: "Shin za ki iya cin amanar mijin ki akan Naira miliyan ɗaya?"
A martanin matar wacce ke shirin amarcewa a cikin wannan watan na Disambar 2020 da muke ciki, ta bayar da amsar cewa "Eh" ga tambayar da aka yi.
An yi rashin sa'a wani da ya san matar ya kuma san wanda ke shirin auren ta, ya ɗauki hoton amsar da ta bayar; wato (screenshot), sannan ya turawa mutumin.
Ganin hakan ne ya tashi hankalin angon har daga bisani ya ce shi ya hakura, ya fasa aurenta.
Ga yadda wata mai amfani da dandalin tuwita ta bayar da labarin; "Wani mutum ya dakatar da daurin aurensa da za'a yi a cikin watan Disamba na shekarar 2020...
saboda amaryar da za'a sha biki da ita ta bayar da amsar cewa za ta iya cin amanar mijinta akan miliyan daya ga tambayar da wani mutum ya yi a Facebook.
"Shi kuma wani mutum da ya san wanda zai aureta sai ya dauki hoton wurin amsar da ta bayar ya nunawa ango....shin wannan mutum ya kyauta? Lagos."
Kalli rubutun;
@smiley_wise hit the follow button...I will follow asap!
— Aunty Canada🇨🇦 (@smiley_wise) December 16, 2020
Source: Legit
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Ango ya dakatar da daurin aure bayan amarya ta yi katobara a 'Facebook'"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?