An dakatar da shugaban kwalejin fasaha bayan gano katafaren gado girke a ofishinsa
Tuesday, 15 December 2020
Comment
Kwalejin kimiyya da fasaha ta Ede ta sanar da dakatar da shugabanta, Adekunle Masopa
Sanarwar dakatar da Masop ta fito ne bayan ziyarar da kwamitin ma'aikatan makarantar ya kai ofishinsa
Kwamitin ya ziyarci ofishin ne domin ganewa idonsa bayan samun korafin cewa Masop ya na sharbar bacci a ofis Hukumar gudanarwa ta kwalejin kimiyya da fasaha (Polytechnic) ta Ede da ke Jihar Osun, ta dakatar da shugaban makarantar, John Adekolawole, bisa zarginsa da kwasar bacci a lokacin aiki, kamar yadda lindaikeji ta wallafa.
Adekunle Masopa, wanda shine shugaban ma'aikata na makarantar (ASUP) ne ya ce sun dauki wannan mataki ne bisa dogaro da dalilai 21 da suke zargin shugaban makarantar da aikatawa.
Da ya ke magana da manema labarai bayan taron gaggawa da kungiyar ta yi, Masopa ya ce suna zargin Adekolawole da rashin girmama ofishinsa na shugaban makaranta tare da sanya makeken gado na alfarma wanda ke ba shi damar yin bacci lokacin aiki.
"Mun gaji da kawo kararsa da ake yi, don haka ne ma'aikatan wannan makaranta suka yanke shawarar ɗaukar mataki na karshe." A cewar shugaban ma'aikatan makarantar.
Ya kara da cewa, "Laifukan da suka janyo ɗaukar wannan mataki sun haɗa da: kauracewa gun aiki har na tsawon wata guda da kuma cin zarafin babban ofishinsa ta hanyar saka gado domin yin bacci."
SOURCE: LEGIT
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "An dakatar da shugaban kwalejin fasaha bayan gano katafaren gado girke a ofishinsa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?