--
Zanga-zanga ya barke a Amurka yayinda Trump yayi zargin magudi

Zanga-zanga ya barke a Amurka yayinda Trump yayi zargin magudi


An fara zanga-zanga a wasu jihohin Amurka yayinda sakamakon zabe ke cigaba da fitowa kuma har yanzu ba'a san wanda zai yi nasara ba, The Cable ta tattaro. A birnin Los Angeles, yan sanda sun damke masu zanga-zanga 40 bayan sun toshe layin dogon jirgin kasa. 


Hukumar yan sandan Los Angeles LAPD ta sanar ta shafinta na Tuwita cewa "Sakamakon wani taron jama'a maras tsari, LAPD na sanarwa jama'a kada su taru a 18th Street da Figuroa." "A daidai wannan lokaci, duk wanda ke wajen ya watse yanzu kuma ya bi umurnin yan sandan." 



Daga baya LAPD ta sanar da ganin mutane 30 a wajen, yayinda aka "damke kimanin mutane 40 da laifin toshe layin dogon jirgin kasa kuma suka ki watsewa." A Seattle, birnin Washington DC, Fox News ta ruwaito cewa an damke akalla mutane takwas suna zanga-zanga. 


Wadanda aka damke sun hada "masu zuba kutsoshi a kan titi." Hakazalika a biranen Raleigh, Oregon da Minnesota, an samu rahotannin zanga-zanga. Har yanzu akwai kishin-kishin rikici yayinda sauran sakamako ke shigowa musamman wadanda aka kada ta akwatin sako.


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

Related Posts

0 Response to "Zanga-zanga ya barke a Amurka yayinda Trump yayi zargin magudi "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?