--
Za a fara biyan haraji kan ko wane burodi a Jihar Kogi

Za a fara biyan haraji kan ko wane burodi a Jihar Kogi

Gwamnatin Jihar Kogi ta bullo da sabon haraji da masu burodi za su rika biya wa kowanne burodi a jihar 


Kungiyar masu gasa burodin ta ce bata goyon bayan harajin don kowa na cikin mawuyacin hali sakamakon Covid 19 


Kungiyar ta ce zata tuntubi wanda aka dora wa alhakin karbar harajin daga hannun 'ya'yanta don samun karin bayani Gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.


 Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida. 

0 Response to "Za a fara biyan haraji kan ko wane burodi a Jihar Kogi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?