
Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umurnin garkame dan majalisar wakilai a kurkuku
Friday, 27 November 2020
Comment
Wata kotun majistare dake Wuse, Zone 6, ta yankewa wani mamban majalisar wakilan tarayya, Victor Mela, hukuncin zama a gidan yari na tsawon wata daya. Amma kotun ta baiwa dan majalisar mai wakitan mazabar Billiri/Balanga, zabin biyan tara.
Rahotanni sun bayyana cewa kotun majistare ta kama dan majalisan da laifin rantsuwa kan karya yayinda yake cika takardan INEC gabanin zaben 2019.
Ya yi rantsuwa har sau uku, cewa shi ba dan wata kasa bane daban yayinda ya mallaki fasfot na Birtaniya. Hukumar yan sanda ta shiga aiwatar da umurnin a Abuja. Karin bayani na nan tafe....
Source: Legit
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umurnin garkame dan majalisar wakilai a kurkuku "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?