--
'Yan bindiga sun sace manyan jami'ai 8 daga tawagar 'yan sanda

'Yan bindiga sun sace manyan jami'ai 8 daga tawagar 'yan sanda


Lauya mai rajin kare hakkin bil'adama, Bulama Bukarti, ya yi tsokaci a kan rahoton da BBC Hausa ta wallafa. - A ranar Talata ne BBC Hausa ta rawaito cewa 'yan bindiga sun sace manyan jami'an 'yan sanda har goma sha biyu a tsakanin jihar Katsina da Zamfara


Labarin sace 'yan sandan bai bayyana ba sai yanzu, bayan kwana goma, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito BBC Hausa sun kawo rahoton cewa ƴan bindiga sun ƙwamushe ƴansanda goma sha biyu dukkaninsu masu muƙamin ASP. 


A cewar BBC Hausa, an sace 'yan sandan ne kwanaki goma da suka gabata bayan 'yan bindiga sun kai wa tawagarsu harin kwanton bauna. Matar ɗaya daga cikin jami'an ƴansandan ita ce wadda ta shaidawa BBC cewa mijinta ya umarceta da ta siyar da gidan da suke zaune don samun kuɗin fansa.Ta ce tasan iyalan sauran jami'ai takwas da aka sace su tare. 


Iyalan jami'an suna ta faman ƙoƙarin haɗa ₦800,000 kowannensu don biyan kuɗin fansa. Lokacin da BBC ta tuntuɓi rundunar ƴansanda reshen jihar Borno, tunda daga nan ne aka tura jami'an, sai suka ce su tuntuɓi rundunar reshen jihar Zamfara ko Katsina. Sai dai gaba ɗayansu wato rundunar jihar Borno, Zamfara da Katsina sun ce basu da wata masaniya dagane da lamarin. 


Lauya mai rajin kare hakkin bil'adama, Bulama Bukarti, ya ce; "abun fargaba ne da razani yadda al-amura ke ƙara ta'azzara a yankin arewa maso yammacin ƙasar nan. 


"Idan har za'a iya ƙwamushe jami'an ƴansanda cikin ayari, to me kuma ya rage, ina makomar sauran karabitin mutane dake zaune kara zube ba tare da makami ko horon kare kansu ba? "Abune a bayyane, haƙiƙa muna wasa da wuta wadda nan gaba zata ƙona mu in har muka yi sake." 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "'Yan bindiga sun sace manyan jami'ai 8 daga tawagar 'yan sanda "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?