--
'Yan bindiga: SSS sun damke mata da miji dauke da harsasai a Katsina

'Yan bindiga: SSS sun damke mata da miji dauke da harsasai a Katsina


Jami'an 'yan sandan farin kaya sun kama wani Usman Shehu da matarsa, Aisha Abubakar da miyagun kaya - Sun kama su ne a wani kauye da ke karamar hukumar Rimi a jihar Katsina, a ranar 22 ga watan Nuwamba 


Kakakin rundunar soji, John Enenche ya sanar da hakan a ranar Alhamis a wani taro na sojoji a Abuja Jami'an tsaro na farin kaya na jihar Katsina sun damki wani miji da matarsa da miyagun makamai. Ana zargin Usman Shehu da matarsa Aisha Abubakar da ta'addanci. 


Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron da sojoji suka yi. A cewarsa, an kama wadanda ake zargin a kauyen Abukur da carbi 14, caliber ammunition rounds 61 na 9.6mm da special ammunition rounds 399 na 7.62m


A cewarsa: "Rundunar soji sun kara samun wata nasara a ranar 22 ga Nuwamban 2020, inda 'yan sanda masu fararen kaya na jihar Katsina suka damki wani Usman Shehu da matarsa Aisha Abubakar, a karamar hukumar Rimi da ke jihar Katsina. 


"Jami'an tsaron sun yi kacibus da 'yan ta'addan a daidai kauyen Abukur, suna dauke da miyagun makamai masu dumbin yawa. An kama su da magazines 14, rounds 61 na 9.6mm caliber ammunition da rounds 399 na 7.62mm special ammunition." 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "'Yan bindiga: SSS sun damke mata da miji dauke da harsasai a Katsina "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?