
Yadda 'yan sandan suka kama wani da ya nemi basu toshiyar baki na N250,000 a Zamfara
Thursday, 26 November 2020
Comment

'Yan sanda sun kama wani da suka yi zargin ɓarawon mota ne bayan ya yi yunkurin basu cin hancin ₦250,000 - Mutumin dan asalin Gidan Dare da ke Jihar Sokoto ya yi yunkurin ba wa yan sanda cin hanci bayan ya gaza ba su gamsassun bayanai kan motar da ya ke ciki
Da ake bincike, ya ce wani dan uwan harkallarsa Abdullahi ne ya sato motar ranar 15 ga Nuwamba 2020 'Yan sandan jihar Zamfara sun kama wani da ake zargin hatsabibin ɓarawon mota ne bayan sun ki karbar cin hancin naira 250,000 daga wajensa kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Mai magana da yawun rundunar, SP Shehu Muhammad, shi ne ya bayyana haka lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Gusau ranar Talata.
"Wanda ake zargin ya kasa gabatar da bayanai masu amfani ga jami'an da suke aiki kuma yayi kokarin biyan su naira 250,000 don kada su kama shi, wanda hakan yasa yan sandan suka tsananta zargi a kansa,"
a cewar Muhammad. Lokacin bincike, wani dan uwan harkallar sa, mai suna Abdullahi, da ke zaune a Abuja, shi ne ya sato motar ranar 15 ga Nuwambar 2020.
SOURCE: LEGIT.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Yadda 'yan sandan suka kama wani da ya nemi basu toshiyar baki na N250,000 a Zamfara"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?