--
Wani dan shekara 69 ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka

Wani dan shekara 69 ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka


Wani dan kasar Amurka ya ce ya saki matarsa saboda ya gano da jefa wa Joe Biden kuri'a yayin zaben shugaban kasa na 2020 


Mutumin da ya yi ikirarin cewa shekarunsa 69 ya ce sun kwashe shekaru 30 suna zaman aure da matarsa amma ba zai iya cigaba da zama da ita ba 



Ya yi ikirarin cewa magudi aka tafka a zaben don haka zai tafi kasar Columbia kuma ba zai dawo ba har sai Amurka ta gyaru 



Wani mutum mai shekaru 69 ya yi ikirarin cewa ya saki matarsa da suka kwashe shekaru 30 suna zaman aure kawai don ya gano ta zabi dan takarar jam'iyyar Democrat, Joe Biden a zaben shugaban Amurka na 2020. 


Mutumin ya kuma yi ikirarin cewa zai tattara komatsansa ya yi hijira zuwa kasae Columbia kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter mai suna @Blanko_b7 kamar yadda LIB ta ruwaito. 


Ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke martani a kan rubutun da Joe Biden ya wallafa kan shirinsa na yaki da annobar Covid 19. 


A cewarsa, ya gama saka hannu kan takardun raba auren kuma 'an kammala komai'. Ya kara da cewa ya yi takaicin ganin cewa sun yi shekaru 30 suna tare da matarsa. 


Har wa yau, ya kara da cewa ba zai dawo Amurka ba har sai an gyara kasar. 


SOURCE: Legit

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Wani dan shekara 69 ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?