--
Turmi da tabarya: Matashi mai shekaru 19 ya mutu a kan karuwa a Legas

Turmi da tabarya: Matashi mai shekaru 19 ya mutu a kan karuwa a Legas


Wani yaro mai shekaru 19 ya mutu dare-dare a kan karuwa - Yaron ya gayyaci karuwar wani babban Otal da ke jihar Legas 


Suna tsaka da sheke ayarsu sai taji shi shuru, ashe ya mutu Wani yaro mai shekaru 19 mai suna Maduabuchi Okeke, ya mutu yana tsaka da lalata da wata karuwa a wani Otal da ke Surulere a jihar Legas.



Kamar yadda shafin Linda Ikeji suka ruwaito, wani dan sanda ya ce Okeke ya dauki wata karuwa mai suna Sandra zuwa wani katafaren Otal da ke layin Ayilara da daddare, suna cikin lalata Okeke ya mutu dare-dare a kan Sandra. 


Kamar yadda rahotonni suka bayyana, bayan Sandra ta fahimci Okeke ya mutu suna cikin lalata, sai ta lallaba waje ta nemi wasu jami'an tsaron Otal guda 2, wani Ottah Nduka da Aliu Tiwalola, suka fitar da gawarsa zuwa harabar Otal din. 


Kamar yadda rahotonni suka kammala, "Wani Maduabuchi Okeke, mai shekaru 19, ya mutu suna tsaka da lalata da wata karuwa, mai suna Sandra, wacce take karuwanci a Otal din Exclusive Mansion."


 Jami'an tsaro guda 2 daga Otal dinne suka dauki gawar suka kai wa wani NasoNaso, sun ce za su kasheshi matsawar ya bai wa wani labarin yadda saurayin ya mutu. An kama karuwar da jami'an tsaron guda 2 don a san asalin abinda ya janyo mutuwarsa, kafin a bai wa 'yan uwansa gawarsa don a birne shi. 


SOURCE: LEGIT

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

Related Posts

0 Response to "Turmi da tabarya: Matashi mai shekaru 19 ya mutu a kan karuwa a Legas "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?