
Tsohon mai mulki ya koma tura amalanke, ya sanar da banbancin mulkin yanzu da wancan zamani
Wani tsohon mutum wanda aka gan shi yana tura amalanke na abincin dabbobinsa ya ce tsohon kansila ne shi - Anibaba ya ce a lokacin mulkin Babangida, N500 ne albashinsa duk da N444 suke tafiya dashi saboda haraji
Ya ce albashinsu ba shi da yawa a lokacin, amma kuma ayyukan da suke yi suna da matukar yawa Wani mutum mai suna Anibaba, ya bayyana yadda ya rike kujerar kansila a jihar Legas lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida.
Anibaba ya ce ya rike kujerar kansila a jihar Legas, inda aka ganshi yana tura amalanke da abincin shanu a ciki. A cewarsa, albashinsa lokacin yana kansila N500 ne, amma ana cire haraji, inda yake tafiya gida da N444 a matsayin albashinsa.
Ya ce a lokacinsu ne aka kirkiri karamar hukumar Eti-Osa. Gabadaya Ajah tana da kansila daya tal ne, sannan Obalende mazaba guda daya ce. Ba wannan bane dan siyasa na farko da ya fara bayyana banbanci tsakanin mulkin wannan zamanin da na da ba.
0 Response to "Tsohon mai mulki ya koma tura amalanke, ya sanar da banbancin mulkin yanzu da wancan zamani "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?