--
Takardun bogi: Kotu ta hana dan takarar APC fitowa zaben maye gurbi na sanatoci

Takardun bogi: Kotu ta hana dan takarar APC fitowa zaben maye gurbi na sanatoci


Babbar kotun tarayya da ke zama a Yenagoa ta dakatar da dan takarar sanatan Bayelsa ta yamma daga tsayawa takara a zaben sanatoci da ke gabatowa - Ta ce shekarun Peremobowei Ebebi na takardun makarantarsa da na katin zabensa da ya gabatar wa INEC su na da banbanci, bata yarda da ingancinsu ba 


 Bisa wannan dalilin ne taki yarda da ingancin takardunsa, don haka ta hana shi takara kwata-kwata Babbar kotun tarayya da ke zama a Yenagoa ta hana Peremobowei Ebebi, dan takarar sanata a karkashin jam'iyyar APC na Beyelsa ta yamma, 


takara a zaben jihar da ke gabatowa. Daily Trust ta ruwaito yadda Alkali Jane Iyang ya yanke da wannan hukuncin a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba, a kan matsalar ha'inci, wanda Richman Samuel, tsohon darektan harkokin cikin gida na gidan gwamnati da ke Yenagoa, ya gabatar a gaban kotu a kan dan takarar APC din. 


Jaridar Legit.ng ta tattaro bayanai a kan yadda kotu ta tabbatar da rashin cancantar Samuel a matsayin dan takarar APC na zaben da ke tunkarowa.


Kotu ta tabbatar da rashin ingancin takardun makarantar Samuel da katin zabensa da ya gabatar ga INEC. Inda alkalin yace shekarunsa na katin zaben da ya gabatar wa da INEC suna da bambanci da na takardun makarantarsa. Har yanzu dan takarar bai riga ya ce komai ba, amma wani dan kungiyar kamfen dinsa ya roki kotu da tayi sassauci a kan hukuncin da ta yanke. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Takardun bogi: Kotu ta hana dan takarar APC fitowa zaben maye gurbi na sanatoci "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?