
Sojan Najeriya ya zane budurwa a kan shigar banza, ya aske ladabtar da matashi saboda askin kansa
Sojoji suna aske gashin kan maza masu tara gashi da kuma zane mata masu damammun tufafi a Ibadan - A yau ne aka wayi gari ana ganin bidiyoyin hakan yana ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani - Sojojin sun tsaya ne daidai wurin Beere da ke cikin babban birnin jihar Oyo suna wannan aikin a bisa umarnin gwamnan
Sojoji suna zane mata masu shigar banza da kuma maza masu tara gashin kai a wuraren Beere da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo, jaridar Daily Nigerian ta wallafa. Idan baku manta ba, sakamakon guguwar zanga-zangar EndSARS a jihar,
Gwamna Seyi Makinde, ya nemi sojoji su tsaya wuri-wuri a jihar don kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali. A bidiyon da yayi ta yawo, an ga sojoji da bulalai suna zane mata masu matsatsun riguna da ke bayyanar da surorin su a titin Beere.
An ga wani bidiyo da ke nuna sojojin suna aske gashin maza masu tara gashi. Daya daga cikin wadanda al'amarin ya faru dashi ya wallafa yadda sojoji suka ci zarafinsa kuma suka aske masa gashi.
Matashin mai suna PrimalHubLtd yace: "Barkanmu 'yan Najeriya, na lura sojoji sun rude. Nazo in bayyana muku artabun da muka yi da su a hanyata ta dawowa daga coci wuraren Bodija da ke Ibadan, wanda sai da na biyo ta wurin Beere inda na samu sojojin suna wurin da Gwamna Seyi makinde ya umarcesu da su tsaya.
"Sai da suka daukeni da mari tukunna nayi biyayya ga umarninsu don gudun cin mutunci. Ina mamaki idan tsawon gashi na nuna mutum dan ta'adda ne ko kuma mai laifi ko barawo. Hakika mutanen nan basu da fahimta, amma yakamata a ce an duba kwakwalwar kowanne soja."
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Sojan Najeriya ya zane budurwa a kan shigar banza, ya aske ladabtar da matashi saboda askin kansa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?