
Shehu Sani ya yi wa ɗan majalisar Burtaniya raddi kan cewa Gowon ya wawushe maƙuden kuɗaɗe
Wednesday, 25 November 2020
Comment

Sanata Shehu Sani ya karyata ikirarin da dan majalisar Burtaniya, Tom Tugendhat ya yi na alakanta Yakubu Gowon da wawushe kudin Najeriya - Tugendhat yayin jawabi a majalisar Burtaniya ya yi ikirarin cewa tsohon Shugaban kasa na mulkin Soja Yakubu Gowon ya kashe kudi kimanin rabin na CBN da zai sauka daga mulki
Sanata Shehu Sani ya karyata hakan inda ya ce babu alamar Gowon na da irin wannan arzikin tun daga saukarsa da mulki har zuwa yanzu kimanin shekaru 40 Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya yi wa ɗan majalisar Burtaniya,
Tom Tugendhat's martani kan iƙirarin da ya yi na cewa tsohon shugaban mulkin soja Yakubu Gowon ya bar mulki da kuɗin da kai rabin abinda babban banki CBN ta mallaka. Tugendhat ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan muhawarar yiwuwar hukunta gwamnatin Najeriya kan zargin keta harkokin bil adama yayin zanga zangar #EndSARS.
Shehu Sani ya ce wannan maganar ba gaskiya bane , inda ya ce Gowon ya sauka daga mulki ba tare da alamun ya tara arziki ba kuma ya cigaba da kasance a hakan fiye da shekaru 40 bayan saukarsa daga mulki. Shehu Sani ya yi wannan martanin ne ta shafinsa na Twitter a ranar Talata 24 ga watan Nuwamba.
Ga abinda ya rubuta: "Janar Yakubu Gowon; Iƙirarin 'sata a CBN' ta ministan Afirka na ƙasar Birtaniya wadda Mista James Duddridge ya yi game da Janar Gowon ba komai bane illa tsantsagwaron ƙarya. Gowon ya sauka daga mulki ba tare da alamun yana da arziki ba kuma ya cigaba da zama a hakan fiye da shekaru 40."
General Yakubu Gowon;The claim of ‘looting the CBN’ made by the British Minister for Africa as represented by Mr James Duddridge against Gen Gowon is nothing but outright falsehood.Gowon exited power without any evidence of wealth & that remains,for over four decades after power.
— Senator Shehu Sani (@ShehuSani) November 24, 2020
SOURCE: LEGIT.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Shehu Sani ya yi wa ɗan majalisar Burtaniya raddi kan cewa Gowon ya wawushe maƙuden kuɗaɗe"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?