
Saudiyya ta bada guraben karatu 424 kyauta ga ɗaliban Najeriya
Tuesday, 17 November 2020
Comment

Ofishin jakadancin Saudiyya ya yaba da irin kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da Najeriya da sauran kasashen Afirka Masarautar Saudiyya ta ce zata bada guraben karatu kyauta ga daliban Najeriya 424 don yin karatu a bangarori daban daban a jami'o'in Saudiyya.
A wata sanarwa da ofishin jakadancin Kasar ya fitar a Abuja, ranar Litinin, ta ce guraben na cikin 6,597 da Saudiyya ke bawa daliban Afirka.
Sanarwar ta kuma ce, ana bawa daliban Jamhuriyyar Benin guraben karatu kyauta 150 duk shekara. "Domin sanin hanyar da za a bi da kuma abubuwan da ake bukata don neman gurbin kyautar karatun, dalibai su nemi bayanai daga ma'aikatar harkokin kasashen waje da kuma ma'aikatun ilimin kasashen su.
Za kuma a iya samun bayani daga ofishin jakadancin Kasar Saudiyya. "Ofishin jakadancin ya kuma yaba da irin kyakkyawar alakar dake tsakanin Saudiyya da Najeriya da kuma sauran kasashen Afirka," a wani bangare na sanarwar.
SOURCE: LEGIT.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Saudiyya ta bada guraben karatu 424 kyauta ga ɗaliban Najeriya"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?