--
Sanata Ladoja ya mayarwa Obasanjo martani kan batun tsige shi a matsayin gwamna a 2006

Sanata Ladoja ya mayarwa Obasanjo martani kan batun tsige shi a matsayin gwamna a 2006


Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja ya yi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo martani kan jawabin da ya yi game da tsige shi a 2005 


 Obasanjo a ranar Alhamis 5 ga watan Nuwamba ya yi ikirarin cewa an tsige Ladoja ne don ya ki yi wa marigayi Lamidi Adedibu ɗa'a 



 Sai dai Ladoja ya bayyana kalaman na Obasanjo a matsayin tsantsagwaron karya mara tushe Tsohon gwamnan Jihar Oyo, Sen. Rashidi Ladoja ya bayyana a jiya cewa labarin da tsohon shugaban kasa Obasanjo kan dalilin tsige shi a shekarar 2005 ba gaskiya bane, 



inda ya kara da cewa Obasanjo bazai iya wanke kansa daga tsigewar da aka masa ba. Ya shawarci tsohon shugaba Obasanjo da kada ya dawo da abu baya saboda ba wani da zai yi ya zare hannunsa daga tsigewar da akayi masa a 2005. 


Obasanjo ya yi jawabi a wajen taron kaddamar da littafin tsohon Gwamna Adebayo Alao-Akala a Ibadan, inda ya bayyana cewa yadda Ladoja ya kasa yi wa marigayi Lamidi Adedibu da Cif Yekini Adeojo ɗa'a hakan yasa aka tsige shi.


 An dai tsige Ladoja daga gwamnan Oyo a shekarar 2005, inda mataimakin sa, Aloa-Akala, ya ci gaba da riqe kujerar, har zuwa lokacin da kotu ta dawo masa da mukamin sa bayan wata sha ɗaya ba tare da mulkin ba. 


Da yake maida martani ta hannun mai yada labaransa, Alhaji Lanre Latinwo, Ladoja ya ce maganar Obasanjo "tsantar ƙarya ne kurum" 


"Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya manta cewa babbar kotun kasa ta yanke hukuncin cewa tsigewar da aka yi wa Ladoja haramtacciya ce." 


Bari mu fadawa Obasanjo gaskiya, shure shuren kaza baya hana mutuwarta, duk wani batancin da zai yi bazai taimake shi ba. Ya kuma ce tsufa ce ta fara saka Obasanjo manta wasu abubuwan. 


"Saboda haka, Ladoja baida wata nadama, yazo ya yi mulki ne gwargwadon iyawarsa, kuma sakamakon hakan ya samu ƙaunar da mutanensa keyi masa har zuwa yanzu," Latinwo ya faɗi a jawabinsa 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Sanata Ladoja ya mayarwa Obasanjo martani kan batun tsige shi a matsayin gwamna a 2006 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?