
Ruhi mai tsarki: Miji ya saki matarsa saboda ta hana ya sadu da ita
Miji ya nemi a raba auransu da matarsa saboda ta hana ya yi mu'amalar aure da ita - A cewar mijin, fasto din matarsa ne ya hana ta tara da shi saboda wai tana dauke da cikin ruhi mai tsarki
Ya zargi matarsa da jin maganar fasto din fiye da nashi duk da cewar a karkashinsa ta ke Wani magidanci da ya gaji da halin matarsa na hana masa hakkinsa na auratayya bisa hujjar cewa tana dauke da cikin ruhi mai tsarki, ya nemi a raba aurensu.
Mutumin wanda ya kasance dan kasar Zambiya ya yi ikirarin cewa tun watan Yuli rabon da matarsa ta bari ya kusanceta da sunan auratayya.
Ya ce tana hana shi hakkinsa saboda wani manzo na coci da take tuntuba tun a shekarar 2018 ya fada mata cewa kada ta yarda ta hada gado dani domin tana dauke da cikin ruhi mai tsarki wanda ake kira da “Holy Spirit” a turance, jaridar The Nation ta ruwaito.
mutumin ya yi zargin cewa matarsa mai shekaru 38, ta fi jin maganar limamin cocin fiye da nashi, sannan cewa a duk lokacin da ya nemi hakkinsa na aure sai ta tuntube shi.
A gefe guda, wani al'amari mai firgitarwa ya faru a jihar Benue, inda wani Nicodemus Nomyange, mai shekaru 40 da haihuwa, ya banka wa kansa da budurwarsa, Shinnenge Pam, wuta, a anguwar Inikpi. The Nation ta ruwaito yadda Nomyange,
wanda yake da yara kuma ya jima yana soyayya da Pam na wani lokaci, ya bukaci aurenta. Rahotanni sun nuna yadda Pam ta watsa masa kasa a ido, inda ta ki amince da tayin aurensa, a cewarta ta gwammaci auren mutumin da bai taba aure ba.
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Ruhi mai tsarki: Miji ya saki matarsa saboda ta hana ya sadu da ita "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?