
Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu
Jaruma Rahama Sadau ta karyata rahotannin cewa an kama ta an kuma gurfanar da ita a gaban kuliya - Jarumar ta ce bata san daga inda labarin ya fito ba kuma ta bukaci masu mata fatan alheri su sani cewa tana nan lafiyarta kalau ba a kama ta ba
Rahama ta yi kira ga masu watsa labaran karyar suyi hakuri su dena don hakan ba komai zai haifar ba sai tada zaune tsaye Rahama Sadau, fitacciyar jarumar fina finan hausa, a ranar Talata 10 ga watan Nuwamban shekarar ta karyata rahotanni da suke yawo a kafafen watsa labarai
na cewa rundunar 'yan sanda ta kama ta kuma za a gurfanar da ita a kotu. Rahama Sadau ta bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar ta Talata.
"An aiko min sakonni da dama na cewa an kama ni kuma an yanke min hukuncin zaman gidan gyaran hali a yau. Ban san daga inda wannan labaran suka fito ba. Don haka, ina kira ga mutane su dena watsa labaran karya marasa tushe.
"Ban samu gayyata daga 'yan sanda ko kotu ba. Ina son jadaddawa masu min fatan alheri cewa ina nan lafiya ta kalau kuma ba a gurfanar da ni a kotu ba. Ga wadanda ke kokarin tada zaune tsaye kan wannan batun, don Allah ku dena...!!!
I haven’t received any police invitation or court trial. I'm reiterating this to well wishers that I’m SAFE and FINE and I have never received any legal trial for whatever reason. To those trying to bank on this issue to create an unrest, Please give it a rest..!!! 😢🙏🏻
— Rahama Sadau 🇳🇬 (@Rahma_sadau) November 10, 2020
SOURCE: Legit
0 Response to "Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?