--
Najeriya ta fi karfin Buhari, ba zai iya ba; Kalaman Dattijo Dakta Junaid

Najeriya ta fi karfin Buhari, ba zai iya ba; Kalaman Dattijo Dakta Junaid

 Batun kisan manoma 43, da mayakan kungiyar Boko Haram suka yanka, ya tayar da hankulan jama'a Jama'a da dama, musamman 'yan arewa, sun mamaye dandalin sada zumunta da alhinin kisan manoman 


Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya matukar APC da Buhari su na kan mulki Tsohon dan majalisa a Jamhuriya ta biyu, Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba matukar shugaba Buhari da APC suna kan mulki. 


A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a ranar Asabar. 


"Na san ya zuwa yanzu 'yan Najeriya sun gaji da labaran kisan fararen hula a yankin arewa maso gabas, musamman a jihar Borno. "Yanzu kuma babu sauran dan Najeriya da bai yarda cewa akwai 'yan bindiga da ke kashe mutane a arewa maso yamma, musamman jihar Zamfara, Katsina, Sokoto, da Kaduna ba. 


"To babu amfani a wurin wannan lusarar gwamnati ta ke aika sakon jaje duk lokacin da 'yan ta'adda suka kashe mutane, ya kamata a ce an wuce wurin da zasu ke fitowa suna cewa kisan fararen hula ya girgizasu. "Duk abin da ya ke faruwa, ya na faruwa ne saboda babu gwamnati a kasar nan. 


"Matukar dai Buhari da APC za su cigaba da zama a gwamnati, ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba, mulkin Najeriya ya fi karfinsa, ba zai iya ba. "Ya fadi kasa warwas, amma saboda munafurci irin na 'yan Najeriya, da kabilanci, da nuna bangaranci, da siyasar addini, 


wasu gani suke Buhari ya na tabuka wani kirki. "Bai tabuka komai ba Kuma babu abinda zai iya yi, idan 'yan Najeriya suna son ganin canji sai su yi wani abu ko kuma su yi shiru, su daina korafi," a cewar Dakta Junaid 


SOURCE: LEGIT

Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

Related Posts

0 Response to "Najeriya ta fi karfin Buhari, ba zai iya ba; Kalaman Dattijo Dakta Junaid"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?