--
Mutanen Gari sun ruguza masallatai 2 saboda sabanin N100 da fasinja a Enugu

Mutanen Gari sun ruguza masallatai 2 saboda sabanin N100 da fasinja a Enugu


Rikici ya barke a garin Nsukka, Enugu, har ta kai an rusa Masallatai biyu - Wasu mutane sun daba wa Direba wuka saboda sabani a kan kudin mota 


Hakan na zuwa ne bayan tsageru sun rusa babban masallacin Orlu a Imo Makonni biyu da kona babban masallacin garin Orlu a jihar Imo, an sake kona wasu masallatan a jihar Enugu, Muslim News ta bada rahoto wannan. 


Jaridar ta ce an kona wadannan masallatai ne a garin Nsukka, Enugu da ke Kudancin Najeriya. Yayin da ‘yan kungiyar IPOB ne ake zargi da laifin kona masallacin garin Orlu, a jihar Enugu ana zargin wasu mutanen gari ne da wannan danyen aiki.


Wannan lamari ya auku ne a ranar 31 ga watan Oktoba, 2020, an kada babban masallacin da ke kan titin Edem da kuma masallacin da ke hanyar bariki. Duka wadannan dakunan ibada su na cikin garin Nsukka ne a jihar Enugu. 


An kona masallacin titin Edem kurmus, sannan aka rusa na hanyar barikin sojoji. ‘Yan kungiyar Keke Riders na direbobin Keke Napep ne da wasu matasa su ka taru su ka yi raga-raga da wadannan manyan masallatai biyu da ke jihar. 


Fauziyat Ida Idoko ta gidauniyar Jaiz Foundation ta ce lamarin ya auku ne bayan an samu sabani tsakanin wata musulmar fasinja da direbobin keke napep.


Wannan Baiwar Allah ta tare keke napep dauke da N150, inda aka fada mata cewa zata biya N250 kafin a kai ta inda za ta sauka, da aka isa sai ta bada N150. A dalilinhaka rikici ya barke har ‘yanuwanta su ka zo, ana haka ne sai wani ya daba wa direba wuka. 


Nan take aka sheka da shi zuwa wani asibiti a Nsukka. Daga nan ne aka zuzuta labarin ana cewa direban ya mutu. Wannan ya sa mutanen garin Enugu su ka rika kai wa musulmai hari, har aka kona masa masallatai. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Mutanen Gari sun ruguza masallatai 2 saboda sabanin N100 da fasinja a Enugu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?