--
Muneerat Abdulsalam ta samu tallafi daga wata kungiya, za ta ga likitan kwakwalwa

Muneerat Abdulsalam ta samu tallafi daga wata kungiya, za ta ga likitan kwakwalwa


Malamar mata, Munirat Abdulsalam, ta samu tallafi daga kungiyar mata Women in Da'awah - Ta bayyana cewa, kungiyar ta bata naira dubu talatin domin karfafa kasuwancinta da kuma ganin likitan kwakwalwa 


Ta yi kira ga jama'a da su kiyayi hantara tare da cin zarafin fitattun jama'a a kafafen sada zumunta Fitacciyar malamar mata, mai bayani a kan zamantakewar aure, Munirat Abdulsalam ta samu tallafi daga kungiyar Women in Da'awa. Kamar yadda Legit.ng ta samu tattaunawa da ita, ta bayyana cewa kungiyar ta shiga matsananciyar damuwa a kan lamarin da ya faru a makonni kadan da suka gabata. 


Idan za mu tuna, Munirat Abdulsalam ta wallafa wani bidiyo inda ta sanar da ficewarta daga addinin Musulunci sakamakon tsangwama, barazana ga rayuwa da sauran hantara da take fuskanta daga jama'a. 


Malamar matan, ta ce suna cikin sahun gaba da suka fara tuntubarta tare da son sanin damuwarta tun bayan aukuwar lamarin. A ranar Juma'a da ta gabata, Munirat ta wallafa wani hoto da ke nuna shigar kudi har naira dubu talatin asusun bankinta tare da sakon godiya ga kungiyar. 


A yayin da Legit.ng ta tuntubeta, ta tabbatar da cewa kungiyar Women in Da'awah ce ta turo mata tare da bukatar ta je ganin likitan kwalkwalwa sannan kuma ta karfafa kasuwancinta. 


Daga bisani, fitacciyar malamar matan ta bukaci jama'a da su dinga bai wa juna uziri tare da tausayawa a rayuwa. Ta roki jama'a da su kiyayi cin zarafi tare da caccakar jama'a a kafar sada zumuntar zamani. 


"Akwai fitattaun jama'a da irin wannan cin zarafin yayi ajali. Ba ku san wanne hali mutum yake a rayuwar shi ba. A dinga bai wa juna uziri tare da tausasawa juna," a cewarta. 



SOURCE: LEGIT

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Muneerat Abdulsalam ta samu tallafi daga wata kungiya, za ta ga likitan kwakwalwa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?