--
Minista Musulmi a Daular Larabawa ya goyi bayan kalaman shugaban Faransa

Minista Musulmi a Daular Larabawa ya goyi bayan kalaman shugaban Faransa


Ministan ma’aikatar harkokin wajen daular Larabawa, Anwar Gargash ya goyi bayan Shugaban kasar Faransa kan cewa akwai bukatar addinin Musulunci ya tafi da tsarin al’ummar Yammacin Duniya - Anwar ya ce Macron baya son ya mayar da al’ummar Musulmi saniyar ware a Yammacin Duniya ne kuma cewa maganarsa na kan hanya 


Ya kuma yi watsi da ikirarin cewa Shugaban Faransa na son mayar da al’ummar Musulmin da ke zaune a Faransa saniyar ware Rahotanni sun kawo cewa wani ministan daular Larabawa, UAE, Anwar Gargash, ya bukaci al’umman Musulmi da su amince da matsayar Shugaban kasar Faransa, 


Emmanuel Macron game da cewar akwai bukatar addinin Musulunci ya tafi da tsarin zamantakewa. Gargash ya bayyana hakan ne yayin zantawa da jaridar Jamus a makon da ya gabata kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito. 


Matsayin ministan na zuwa ne a yayinda ake gudanar da zanga zanga a kasashen Musulmi domin Allah-wadai da kalaman Macron a kan addinin Musulunci, bayan ya zargi Musulmi da wariya. 


Hakazalika Shugaban na Faransa ya kuma kare wani zanen batanci ga Annabi Muhammad (SAW) wanda ya haddasa cece kuce a duniyar Musulmi. Ministan ya ce: “Ya kamata Musulmai su bude kunnuwansu da kyau su saurari abin da Macron ya fada a jawabinsa. 


“Baya son ya mayar da al’ummar Musulmi saniyar ware a Yammacin Duniya, kuma maganarsa tana kan gaba.” Ya ci gaba da cewa Musulmai na bukatar “su saje da tsarin da ya fi na yanzu” a kasashen Yammacin Duniya. 


“Faransa na da hakkin zakulo hanyoyin da za a cimma hakan ta yadda za a yaki tsaurin ra’ayi da kuma gidadanci,” inji shi. Gargash ya yi watsi da zargin cewa Macron yana so ne ya mai da al’ummar Musulmin da ke zaune a Faransa saniyar ware. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Minista Musulmi a Daular Larabawa ya goyi bayan kalaman shugaban Faransa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?