
Maza ne suka tarwatsa rayuwata, mahaifiyar 'ya'ya 4 daga maza daban-daban
Wata mata 'yar kasar Ghana ta bayyana yadda ta yi ta yaudarar kanta tana tunanin maza za su kula da ita Maza 4 suka yaudareta duk ta haifa musu yara, amma suka juya mata baya suka barta da wahalar duniya
Yanzu haka kwana take yi a shagon wani mutum tare da yaranta 4, cikin yunwa da kuncin rayuwa Sophia Koji, wata mata 'yar kasar Ghana mai shekaru 31, ta bayyana yadda tayi ta yaudarar kanta, tayi tunanin maza za su iya kula da ita.
Kamar yadda matar ta bayyana a Crimecheckfoundation.org, tana da yara 4 wadanda ta haifa da maza daban-daban. Maimakon mazan su kula da ita da yaran, sai suka bar ta tana fama da wahalhalun rayuwa. Sophia ta bayyana yadda ta koma kwana a shago, ita da yaranta sannan suka yi ta fama da yunwa da kishi saboda ta rasa kudaden shiga.
A cewarta, "Akwai mutumin da nake tsarewa shago, duk ranar da ba mu yi ciniki ba za mu zauna da yunwa, ina bai wa wanda nake yi wa aiki kudaden. "Ko da na gama siyar da kaya, sai ya ga dama zai biya ni.
Akwai lokacin da ya bukaci yayi lalata dani, naki amincewa, tun daga nan ya fara cutar dani. "Bayan na samu labarin Crime Check Foundation wadanda suke bai wa mata masu yara GHc 500 don su taimaka wa yaranta."
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Maza ne suka tarwatsa rayuwata, mahaifiyar 'ya'ya 4 daga maza daban-daban "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?