--
Labari mai zafi: Yau Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli zai san halin da rawaninsa ya ke ciki

Labari mai zafi: Yau Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli zai san halin da rawaninsa ya ke ciki


A ranar Juma’a ne kotun Dogarawa za ta saurari shari’ar nadin Sarkin Zazzau - Iyan Zazzau ya na kalubalantar nadin da za ayi wa Amb. Ahmad Nuhu Bamalli 


Bashir Aminu ya roki kotu ta dakatar da bikin nadi da kuma mika sandar girma Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa a ranar 6 ga watan Nuwamba, 2020, 


babban kotun jihar Kaduna zai saurari shari’ar nadin sarkin Zazzau,. Wannan kotu da ke zama a Zaria, jihar Kaduna, zai saurari karar da daya daga cikin Sarakan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu ya shigar a gabansa.


A ranar Laraba, kotu ta saurari Lauyoyi masu shigar da kara da kuma masu kare wanda ake zargi. 


Bayan an yi zama a ranar 4 ga watan Nuwamba, Alkali mai shari’a Kabir Dabo ya dage karar zuwa yau, ya ce a ranar Jum’a kotu za ta yanke hukunci.


 Iyan Zazzau, Aminu ya roki Alkali ya bayyana shi a matsayin sabon Sarkin Zazzau, sannan ya yi fatali da nadin da gwamnati ta yi wa Ahmad Bamalli. 


Lauyoyin Bashir Aminu sun kuma nemi alfarmar kotu a dakatar da bikin nadin sabon Sarkin Zazzau, sannan a hana mika wa Sarkin sandar girma. 


Iya ya shigar da kara ne ta hannun Ustaz Yunus SAN a kotun da ke Dogarawa, Sabon Gari, Kaduna. 


Idris Aliyu shi ne Lauyan da ya tsayawa gwamna da sakataren gwamnati da kwamishinan shari’ar Kaduna, ya kuma kare gwamnati a zaman da aka yi.


Daily Trust ta ce Lauyan da ya tsaya wa kwamishinar harkar masarautu shi ne Kenechukwu Azioyo. Lauyoyin sun roki ayi fatali da karar babban basaraken. 


Za ku tuna tsohon hakimin sabon Garin ya na ikirarin masu nadin sarki sun mika wa gwamna Nasir El-Rufai sunansa a matsayin magajin Shehu Idris. 


Mutane 10 ake kara a a wannan shari'a, daga ciki har da asir El-Rufai, babban Lauyan jihar Kaduna; Majalisar Sarakunan Kaduna; Majalisar Masarauta. Sauran su ne: 


Wazirin Zazzau, Fagacin Zazzau, Makama Karamin Zazzau, Limamin Juma'an Zazzau, da Mai martaba Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Labari mai zafi: Yau Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli zai san halin da rawaninsa ya ke ciki "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?