
kuɗaɗen ceto: Gwamnatin ta sauya adireshin yanar gizo na neman tallafin ƙanana da matsakaitan sana'o'i
Tun a cikin watan Satumba gwamnatin tarayya ta bude shafin yanar gizo domin jama'a su nemi tallafi daga kudaden ceto, N75bn, da aka ware - Sai dai, al'amura sun ki tafiya yadda ya kamata tun bayan bude shafin tare da sanar da jama'a adireshinsa domin su nemi tallafin
Gwamnatin tarayya ta ce ta sauya adireshin shafin kuma zai koma kan sabon turken yanar gizo daga ranar 1 ga watan Nuwamba Gwamnatin tarayya tace za ta sauya adireshin yanar gizo na shafin neman tallafin Ƙanana da matsakaitan sana'o'i (SMEs survival fund) da kuma tsarin Guaranteed off-take Stimulus
Scheme daga 1 ga watan Nuwamba. A cewar gwamnati, ta yi hakan ne sakamakon ƙalubalen gudarnarwa da suke fuskanta a kan adireshin farko da aka turke shafin a kansa a yanar gizo.
Ambasada Maryam Katagum, Ministar Kasuwanci da massna'antu kuma shugabar kwamitin tsarin tallafin ceton ƙanana da matsakaitan sana'o'i (MSME survival fund) da kuma Guaranteed off-take Stimulus Scheme, ita ce ta bayyana hakan ranar Asabar a garin Abuja.
Acewar ministar, adireshin yanar gizon na neman tallafin zai sauya matsuguni zuwa www.survivalfund.gov.ng daga ranar 1 ga watan Nuwamba.
"Ina mai sanar da kafatanin al-umma, sakamakon matsalar gudanarwa, kwamitinmu zai sauya adireshin yanar gizo na neman tallafin kanana da matsaikaitan sana'o'i daga ranar 1 ga watan Nuwamba zuwa www.survivalfund.gov.ng
"Ana gargaɗin jama'a cewa kada su bawa kowa kudinsu da sunan zai taimaka musu don cin moriyar tallafin," a cewar ministar yayin da take tabbatarwa da jama'a cewa komai kyauta ne.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa survival fund tallafi ne don ceton wanda annobar Korona ta shafa a kanana da matsaikaitan sana'o'in su, don farfaɗo da sana'o'i da da ceto ayyuka da rage radaɗin karyewar tattalin arziƙin kasuwan da 'yan kasuwa.
A yayin ranar 27 ga watan Oktoba ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta sanar da kaddamar da shirin bunkasa tattalin arziki ta hanyar fara bayar da tallafin N30,000 ga mutum 300,000 a jihohi 10.
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "kuɗaɗen ceto: Gwamnatin ta sauya adireshin yanar gizo na neman tallafin ƙanana da matsakaitan sana'o'i "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?