
Ku mayar da hankali kan matsalolin kasa ba Rahama Sadau ba - Reno Omokri
Reno Omokri ya caccaki 'yan arewa a kan yadda suka yi ta sukar Rahama Sadau saboda hotunan tsiraicinta - Ya ce maimakon su caccaki 'yan siyasa masu satar dukiyar al'umma amma sun mayar da hankali a kan jarumar
A cewarsa, akwai matsaloli da dama da yakamata a ce an mayar da hankali, amma an dage wurin caccakar Rahama Reno Omokri ya yi amfani da shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ya caccaki musulmai a kan zagin Rahama Sadau saboda rigarta mai bayyana tsirarici,
amma suka yi shiru a kan satar da 'yan siyasa suke yi. Reno ya wallafa hotunan musulmai mata da suke wasu kasashen, inda ya rubuta; "Yan Najeriya, wadannan hotunan mata musulmai ne daga kasar Egypt, Pakistan da Lebanon. Kuna tunanin abinda Rahama Sadau ta aikata ya tsananta? Daga Musulunci har addi"Mun saka wa wani filin wasa sunan wani babban barawo.
A wannan jihar dai, an ga gwamna a kamara yana amsar rashawa ta daloli. Bai kamata a ce mu nuna takaicinmu a kansa ba, sai Rahama? "Ta yaya za a ji dadin zaman duniya, idan muka kyale Boko Haram, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma mutane miliyan 13 da basu zuwa makaranta a arewacin Najeriya, amma mun mayar da hankali a kan shigar Rahama Sadau?"
Rahama ta fuskanci caccaka daga mutanen arewa a kafar zumuntar zamani ta Twitter makon da ya gabata, saboda bayyanar hotunanta masu bayyana tsiraicin ta. Yanzu haka hukumar shirya fina-finai ta MOPPAN ta dakatar da ita saboda bayyanar hotunan na ta.
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Ku mayar da hankali kan matsalolin kasa ba Rahama Sadau ba - Reno Omokri "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?