--
Ku dakatar da Buhari daga fita waje domin duba lafiya - Majalisa ta gargadi fadar shugaban kasa

Ku dakatar da Buhari daga fita waje domin duba lafiya - Majalisa ta gargadi fadar shugaban kasa


Majalisar dattijai ta gargadi babban sakataren fadar shugaban kasa a kan su dakatar da shugaba Buhari daga fita ketare domin neman lafiya 


Gargadin majalisar na zuwa a lokacin da babban sakataren fadar shugaban kasa ya gabatar da kasafin fadar shugaban kasa a gaban majalisa 


Fadar shugaban kasa ta gabatar da kasafin kudinta ma shekarar 2021 wanda ya kama N19.7bn A ranar Alhamis ne majalisar dattijai ta gargadi ma'aikatan fadar shugaban kasa (Asorock Villa) su dakatar da shugaba Buhari daga fita waje domin a duba lafiyarsa. 


A cewar majalisar, yin hakan zai tabbatar da cewa asibitin fadar shugaban kasa ya koma hayyacinsa a cikin shekarar nan. 


Kwamitin majalisar dattijai a kan tabbatar da daidaito da alaka a tsakanin bangarorin gwamnati ne ya yi wannan gargadi yayin da babban sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar, ya bayyana a gabansa domin kare kasafi kudin shekarar 2021. 


Fadar shugaban kasa ta gabatar da kasafin kudinta na shekarar 2021 wanda ya kama N19.7bn, 


daga cikin kudin ne kuma aka warewa asibitin fadar shugaban kasa zunzurutun kudi da yawansu ya kai N1.3bn. 


Da ya ke martani a kan kasafin kudin, shugaban kwamitin, Sanata Danjuma La'ah, ya ce kwamitin zai amince da kasafin fadar shugaban kasa amma ya jaddada cewa shugaban kasa da sauran manyan jami'an gwamnati ba zasu kara fita waje domin a duba lafiyarsu ba. 


Da ya ke ganawa da manema labarai bayan gabatar da kasafin kudin, Umar ya dauki alkawarin samar da dukkan kayayyakin duba lafiya da shugaban kasa da sauran manyan jami'an gwamnati ke bukata a asibitin fadar shugaban kasa 


da zarar majalisa ta amince da kasafin kudin da ya gabatar. A wani yunƙurin ƙarawa jami'an ƴansanda himma da karsashi a ƙasa baki ɗaya domin farfaɗowa da sauri daga illolin zanga-zangar #EndSARS,


 babban Sufetan ƴansanda na ƙasa ya ce dukkanin jami'an da suka rasa ransu ko suka jikkata za'a ɗaga darajarsu zuwa matsayi na gaba. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Ku dakatar da Buhari daga fita waje domin duba lafiya - Majalisa ta gargadi fadar shugaban kasa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?