--
Kotu ta bawa CBN izinin saka sakata a asusun masu assasa zanga-zanga a Nigeria

Kotu ta bawa CBN izinin saka sakata a asusun masu assasa zanga-zanga a Nigeria


Tun a cikin watan Oktoba babban bankin kasa ya nemi izinin kotu domin rufe wasu asusun banki 19 - CBN ya nemi izinin rufe asusun ne bisa zargin cewa ana amfani da su wajen rura wutar zanga-zangar ENDSARS 


Zangar-zangar lumana ta ENDSARS da aka fara a wasu biranen Najeriya ta rikide zuwa kazamin rikici Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar babban bankin Najeriya (CBN) na rufe asusun na rufe wasu asusun banki 19 mallakar wasu daidaikun mutane da kamfanonin da aka gano suna da alaka da zanga-zanagar ENDSARS. 


Tun a ranar 20 ga watan Oktoba CBN ta nufi kotun domin neman ta bata izinin rufe asusun 19 amma sai ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba, kotu ta amince da bukatar, kamar yadda rahotanni suka tabbatar. 


Wasu daga jagorin zanga-zangar ENDSARS sun yi korafin cewa an hanasu barin Najeriya a yayin da suka yi niyyar ficewa daga kasa. CBN ya nemi rufe asusun ne bisa zargin cewa wasu mutane da kamfanoni suna amfani da kudi domin rura wutar zanga-zangar ENDSARS. 


Jaridu sun kawo labaran yadda aka dinga walima da rabon kayan kwamal da makulashe a wuraren taron gangami da masu zanga-zangar ENDSARS suka yi a wasu biranen Najeriya. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Kotu ta bawa CBN izinin saka sakata a asusun masu assasa zanga-zanga a Nigeria"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?