--
Kisan Manoma A Borno: A Gabana Aka Yi Ta Yanka ’Ya’yana —Mahaifi

Kisan Manoma A Borno: A Gabana Aka Yi Ta Yanka ’Ya’yana —Mahaifi


Wani magidanci ta ya tsallake rijiya da baya a harin da Boko Haram ta kashe manoma 43 ya bayyana wa Aminiya abin da ya faru da su a hannun mayakan kungiyar.


Malam Abubakar Yunus wanda kungiyar ta kashe ’ya’yansa biyu a harin ya ce tare da shi aka kama su kuma a kan idonsa aka yanka su.


Ya ce suna tsaka da aikin girbin shinkafa na mayakan Boko Haram suk ayi musu kofar rago.


“Mutane na aiki a gonakinsu. A gonarmu abun ya fara ne misalin karfe 10.30 na safe lokacin da mayakan Boko Haram dauke da bindigogi sanye da kayan sojoji suka yi mana kawanya.


“A gabana suka yanka ’ya’yana bayan da daya daga cikin mayakan ya tambaye ni matsayin yaran a wurina! Na amsa da cewa ’ya’yana ne.


“Har yanzu ina cikin tashin hankali game da irin wannan rashin imani da aka nuna min”, inji Malam Abubkar.


 


‘An shafe majiya karfin yankin Zabarmari’


Majiyar Aminiya a garin Zabarmari ta kisan gillar ta kusa shafe matasa da majiya karfin yankin.


“Matasa ne majiya karfi da za su kula da wannan al’umma a nan gaba aka yi wa kisan kiyashi.


“Ba za mu taba farfadowa ba saboda karni guda na al’umma ne sukutum aka shafe aka bar mu tsofaffi, mata da kananan yara masu rauni”, inji majiyar.


Wakilinmu ya ce manoma da suka hada da mata da kananan yara, suna taska da girbin shinkafa ne mayakan suka ritsa su da misalin karfe 9 na safe ranar Asabar, a Zabarmari mai tazarar kilimita 25 daga Maiduguri, hedikwatar Jihar Borno.


Sai daga baya a ranar Lahadi aka samu karin bayani game da yadda aka karkashe rukunin farko na manoman.


Rahotanni sun ce sai da mayakan suka tisa keyarsu da bakin bindiga zuwa wani wuri sannan suka rika yi musu yankan rago da fille kai.


Bayan sun karkashe rukunin farko na manoma 43, sai mayakan suka yi ta banka wa gonakin da ke yankin wuta.


Hakan ya hana jami’an tsaro da ’yan sa kai isa ga wurare masu makwabtaka da Zabarmari domin ganin halin da suke ciki, a cewar majiyoyi


SOURCE: AMINIYA DAILY TURST

Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

Related Posts

0 Response to "Kisan Manoma A Borno: A Gabana Aka Yi Ta Yanka ’Ya’yana —Mahaifi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?