
Ke mayya ce idan mijinki ya tsiyace bayan kun yi aure - Malamar Mata
Malamar mata, marubuciya, kuma fasto a Cocin Agape Ministries, Funke Adejomo, ta ce mayun mata sune silar talaucewar maza da yawa - A cewar Funke, zubar da mutunci ne mace ta ke rokon mijinta kudin sayen rigar mama
Funke ta zaburar da mata su tashi domin neman na kansu, su tsaya da kafafunsu, su daina dorawa mazajensu dukkan nauyin rayuwarsu Funke Adejomo, marubuciyar Najeriya kuma fasto a cocin Agape Ministries, ta bayyana cfewa duk macen da arziƙin mijinta ya karye bayan ya aureta, bata da maraba da mayya.
Ta faɗi hakan lokacin da take magana akan irin muhimmiyar rawa da yakamata mata su taka a gidan mazajen su yayin wa'azi a coci. Lokacin da take yin huɗuba,Funke,ta caccaki mata masu bajewa a gidan miji suyi ta haifu ƴa'ƴa kuma su bar mazajensu da wahala.
"Bai kamata ki zamo mara amfani ba,ace sai kin roƙi mijinki ya baki kuɗi kafin ki sai rigar mama.Wannan abubuwa ne da ke zubar da daraja da kuma kimar ƴa mace,'' A cewar Funke. Sannan ta cigaba da cewa; "kada ku ɗorawa mazajenku nauyin ƴayanku don ba nasu bane su kaɗai ya kamata kuma ku bada gudunmawa duk ƙanƙantar ta.
"Kiyi abin kirki da rayuwarki a matsayinki na mace. An halicce ki ne don ki ƙarawa abubuwa armashi. "Na ƙarawa aurena armashi. Mijina da kansa ya kalli cikin idanuna yace ina son na aureki'.Kada ki zama mace mai roƙo.''
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Ke mayya ce idan mijinki ya tsiyace bayan kun yi aure - Malamar Mata "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?