
Karuwa ta kai wa magidanci 'yan sanda saboda ya kwace iPhone 11 da ya siya mata
Wani matashi mai suna Busdor ya bayar da labarin yadda ta kaya tsakanin wani mutum mai aure da budurwarsa - Saurayin ya ce mutumin ya kama budurwar tasa da wani saurayi daban, sai ya kwace wayar da ya siya mata
Ita kuma budurwar ta kira masa 'yan sanda, amma ya ki ba su dama, yace ta rike duk abinda ya siya mata amma banda wayar Wani saurayi mai suna Busdor ya bayar da labarin al'amarin da ya faru tsakanin wani mutum mai aure da matarsa ta ke Ingila, da budurwarsa wacce makwabciyar Busdor ce.
A cewarsa, mutumin ya ziyarci budurwarsa ne sai ya same ta tare da wani saurayin, take a nan ya kwace wayar da ya siya mata. Bayan motarsa ta samu matsala kusa da gidan budurwar, washegari da safe ta kira masa 'yan sanda don su amso mata wayarta.
Mutumin kuwa ya ki bude kofa, a cewarsa yana tare da kananan yaransa kuma tsoro suke ji. Ya ce budurwar ta rike gida da shagon da ya siya mata, amma ba zai bayar da wayar ba.
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Karuwa ta kai wa magidanci 'yan sanda saboda ya kwace iPhone 11 da ya siya mata "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?