
Ina! Ba za ta yiwu ba: Bayan Trump ya yi ikirarin ‘kai labari’, ya koma cewa ‘ana shirin magudi’
Donald Trump ya zargi Jam’iyyar hamayya da kokarin ‘sace zabe’ - Shugaban kasar ya ce wasu sun kada kuri’a bayan an rufe rumfuna
Ana sa ran cewa an jima kadan Trump zai yi wa Amurkawa jawabi Yayin da ake cigaba da sauraron sakamakon zaben shugaban kasa a Amurka, Donald Trump ya fito ya yi jifa da zargi mai karfi a ranar Laraba.
Donald Trump ya na zargin cewa ana kokarin sace masa kuri’u. Shugaban kasar bai bada wasu hujjoji da za su gaskata ikirarin da ya ke yi ba.
Shugaban ya ce an kyale wasu su na kada kuri’a a lokacin da ya kamata ace an rufe rumfuna.
Trump ya bayyana wannan ne a shafinsa na Twitter, Legit.ng ta fahimci cewa Twitter ta yi wa wannan magana tambarin kanshin rashin gaskiya.
“Mu na gaba, amma su na kokarin sace zaben. Ba za mu taba bari su yi wannan ba.” Inji Trump. ‘Dan takarar jam’iyyar Republican din ya cigaba da cewa:
“Ba za a rika kada kuri’a bayan an rufe rumfunan zabe ba.” - inji @realDonaldTrump. Shugaban kasar Amurkan ya fasa wannan kwai ne da kimanin karfe 6:50 a agogon Najeriya. Twitter ta hana a iya maida martani a kan sakon.
Shugaba Trump ya yi alkawarin cewa zai fito ya yi wa mutanen kasar Amurka jawabi na musamman game da sakamakon zaben da ake yi.
Kafin yanzu, Trump ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta na kan nasara a zaben Amurkan. Shugaban kasar ya gode wa jama’an da su ka kada masa kuri’a.
A baya kun ji cewa Shugaba Amurka, Donald Trump ya ji dadin gangamin da wasu Bayin Allah su ka shirya masa a yankin kudu maso gabashin Najeriya.
A shafin Twitter, Trump ya tanka Magoya-bayan na sa daga uwa-Duniya, Ontisha a jihar Anambra
We are up BIG, but they are trying to STEAL the Election. We will never let them do it. Votes cannot be cast after the Polls are closed!
— Donald J. Trump (@realDonaldTrump) November 4, 2020
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Ina! Ba za ta yiwu ba: Bayan Trump ya yi ikirarin ‘kai labari’, ya koma cewa ‘ana shirin magudi’ "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?