
Ikon Allah sai kallo: Bidiyon wani mutum yana rabon fada tsakanin kaji biyu
Bidiyon wani mutumi yayinda yake kokarin raba fada tsakanin kaji biyu ya yi fice a shafin soshiyal midiya - Mutumin ya yi wa kajin fada yayinda ya rike su, sannan ya ture kowannensu gefe
Jim kadan bayan mutumin ya dan matsa sai kajin suka sake far ma junansu da hari yayinda shi kuma ya ci gaba da ture su Wani mai amfani da shafin soshiyal midiya, Tumi Sole ya wallafa bidiyon wani mutumi yana raba fada a tsakanin kaji biyu.
Bidiyon mai tsawon sakwan 30 ya fara ne da nuno mutumin rike da kaji a dukka bangarorinsa biyu na hagu da dama yayinda yake yiwa daya daga cikinsu magana. Sai kuma ya juya kansa don yi wa daya kazan shima fada. Chan kuma sai ya shiga tsakaninsu inda ya sake su.
A nan ne kuma sai fada ya sake barkewa a tsakanin kajin. Ga dukkan alamu dai ba za su iya barin junansu ba.
Sai suka fara caccakar junansu yayinda mutumin ya ci gaba da kasancewa a tsakaninsu. Abun ya bashi haushi yayinda ya fara yi masu ihu.
Kalli bidiyon a kasa:
Mzansi & content!
— Tumi Sole (@tumisole) November 17, 2020
Have a superb Tuesday! đđđđ
Thanks for sharing this @diggiebongz pic.twitter.com/NC53FRkQ8c
Ga wasu daga cikin sharhin da mutane suka yi kan bidiyon:
@CeliShongwe ta wallafa: "Abun da ban dariya sosai, za ka rantse da mutum yake magana.”
@juju_moate ya wallafa: "Kuma suna da fitina.” @itsKamoBruv ya rubuta: "Shakka babu wadannan
@ChickenLickenSA vs @NandosSA ne suke fada a unguwannin Twitter.”
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Ikon Allah sai kallo: Bidiyon wani mutum yana rabon fada tsakanin kaji biyu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?