
Ikon Allah: gawa ta farfado a asibiti a yayin da ake shirin mata sutura
Wani mutum da ya farfado bayan ajiye a dakin gawa ana shirin yi masa sutura - Mutumin Kiplangat Kigen mai shekara 32 ya fadi a gidansa kuma an garzaya da shi asibiti kuma aka yi tsammanin ya mutu a ranar Talata
Hukumomin asibitin suna ci gaba da binciken dalili kai shi dakin adana gawarwaki bayan yana numfashi Wani mai fama da matsananciyar jinya, wanda ya fadi a gidansa da ke Kenya kuma aka garzaya da shi asibiti, ya bawa masu kula da dakin ajiyar gawa mamaki bayan da ya farfado lokacin da ake shirin yi masa sutura.
Peter Kigen, mai shekara 32, an yi tsammanin ya mutu a ranar Talata kuma ma'aikatan asibitin Kapkatet, a yankin Kericho suka maida shi dakin gawa kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Wani mai kula da dakin adana gawar ya ce ya gano mutumin ya na numfashi lokacin da ya taba jikin sa. Mai kula da dakin ne ya mika rahoton gaggawa ga jami'an asibitin aka kuma maida shi sashen bada kulawa ta musamman don ci gaba da ceton rayuwarsa. Wani ma'aikacin asibitin, Gilbert Cheruiyot ya bayyana a ranar Laraba cewa wani mutum mai suna Kiplangat Kigen, mai shekara 32, ya farfado.
Cheruiyot an maida shi sashen kula da masu kowace irin larura kuma yana samun sauki. Ya ce ana ci gaba da binkice don gano dalilin kai shi dakin gawa duk da cewa da ransa. "Muna so musan menene hakikar abin da ya faru har ya sa aka bayyana wani ya mutu bayan ya na raye. Yanzu muna bincike kuma za mu bada gamsashen rahoto," a cewar Cheruiyot.
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Ikon Allah: gawa ta farfado a asibiti a yayin da ake shirin mata sutura"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?