
Idan ajali ya yi kira: Daga satar babur, kotu ta yanke hukuncin rataya ga wani mutum
Satar babur ta janyo kotu ta yanke wa wani dan shekaru 44 hukuncin kisa ta hanyar rataya
An dai gurfanar da Rafiu Saheed ne bisa tuhume-tuhume biyu na kokarin kisan kai da kuma fashi da makami
Saheed ya yanka wani dan achaba da ya dauka haya sannan ya sace masa babur dinsa, sai dai dan achaban bai kai ga mutuwa ba An yanke wa wani mutum mai shekaru 44, Rafiu Saheed,
hukuncin kisa ta hanyar rataya kan aikata fashi da makami da kuma satar babur. An gurfanar da shi a kotu a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2017 kan tuhume-tume biyu na yunkurin kisan kai da fashi da makami.
Lauyan gwamnati daga ma’aikatar shari’a, Bankole Awoyemi, ya fada ma kotun cewa a ranar 30 ga watan Yuli, 2012, Saheed ya yo hayar wani dan achaba,
Olaniyi Olayinka, domin ya kai shi gidan dan uwansa a Ipetumode daga Ile-Ife. Yayinda komawa Ife, Saheed ya fito da wuka sannan ya yanka makokwaron dan achaban, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Mai laifin ya tsere da babur din, bayan ya yi tunanin cewa mai babur din ya mutu amma sai Allah ya raya shi. Daga bisani sai aka kama mai laifin sannan aka kwato babur din daga hannunsa.
Awoyemi ya fada ma kotu cewa laifin da Saheed ya aikata ya yi karo da sashi 6(b) da 1(2)(a) na fashin da makami da kuma sashi na 320 na Criminal Code Law, Cap 34, dokar jihar Osun na 2002.
Da kuma sashi 1(2) na dokar fashi da makami, Cap R11 na dokar tarayyar Najeriya 2004. Saheed bai amsa laifin da ake tuhumarsa a kai ba sannan lauyansa, Julie Olorunfemi, y roki kotu da ta yi sassauci ga wanda yake karewa.
A hukuncinsa, Justis Kudirat Akano, ta yankewa Saheed shekaru 14 a gidan yari kan yunkurin kisan kai da kuma hukuncin kisa ta hanyar rataya na fashi da makami.
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Idan ajali ya yi kira: Daga satar babur, kotu ta yanke hukuncin rataya ga wani mutum "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?