--
Kalli Hotunan kafin auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi da kyakyawar amaryarsa

Kalli Hotunan kafin auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi da kyakyawar amaryarsa

 Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Nuhu Abdullahi na shirin angwancewa - Za a kulla aure tsakanin Nuhu da amaryarsa Jamila Abdulnasir a ranar Juma’a, 4 ga watan Disamba, a jihar Kano 


Jarumin da kansa ya wallafa hotunan kafin aurensu a shafinsa na Instagram Shahararren jarumin nan na Kannywood wanda tauraronsa ke kan haskawa a masana’antar shirya fina-finan ta Hausa, Nuhu Abdullahi na shirin angwancewa. 


Za a daura auren Nuhu tare da amaryarsa Jamila Abdulnasir a ranar Juma’a, 4 ga watan Disamba, a jihar Kano. Tuni dai manyan jaruman masana’antar da shi kansa angon suka fara wallafe-wallafen hotunan kafin auren masoyan biyu. 


A hotunankafin auren nasu wanda Legit.ng ta gano a shafin jarumin na nuhuabdullahi a Instagram, an gano masoyan biyu sanye da kayayyaki na alfarma da kamala. 


A cikin daya daga cikin hotunan, amaryar ta kasance sanye da atamfa launin ruwan kasa da launin ruwan gwal yayinda shi kuma angon ya saka dinkin babbar riga launin ruwan kasa shima. 


A wani hoton kuma, angon ya saka farin shadda dinkin babban riga inda ita kuma sahibar tasa ta sanya dinkin doguwar riga launin ruwan hoda. Sun kuma rike junansu a hoton cike da shauki. Jarumin ya kara shahara sakamakon wani shiri mai suna Labarina da masana’antar ke haskawa a yanzu wanda ya dauki hankalin ma’abota kallon fina-finan Hausa. 


Ga hotunan da ya wallafa a shafinsa na Instagram a kasa :






Ga katin gayyata zuwa wurin daurin auren:





 SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Kalli Hotunan kafin auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi da kyakyawar amaryarsa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?