--
Kalli Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano

Kalli Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano


Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta samu nasarar fasa kwalaben giya 1,975,000 masu kimar naira miliyan 200 - Hukumar ta yi hakan ne cikin shirin dakatar da rashin da'a a jihar, domin giya haramun ce a musulunci 


Gwamnan jihar wanda ya samu wakilcin mataimakinsa ya ce za su tabbatar da inganta albashin hukumar Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta fasa kwalaben giya 1,975,000 mai kimar naira miliyan 200 a cikin tsakiyar jihar Kano, Daily Trust ta wallafa hakan a ranar Lahadi. 


Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Nasiru Gawuna, yayin fasa kwalaben giyan a Kalebawa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa, ya ce shan giya zai iya janyo matsala ga kwakwalwar mutum, sannan Musulunci ya haramta. 


Gawuna ya ce daya daga cikin rawar da mulkinsu zai taka shine tabbatar da walwalar 'yan Hisbah kafin karshen 2020, za a tabbatar an kara musu albashi sannan an samar mu su da sababbin kayan aiki. "Mulkina yana alfahari da yadda ku ke jajircewa a kan ayyukanku. 


Don haka za mu yi iyakar kokarin ganin mun ba ku kwarin guiwa don cigaba da ayyukanku," cewarsa. A jawabin kwamanda janar na hukumar Hisbah, Sheikh Harun Muhammad Ibn Sina, ya ce hukumar ta samu nasarar lalata motoci 20 wadanda suke makil da giya. 


Yayin da Ibn Sina ya bayyana farin cikinsa a kan yadda gwamnatin jihar take basu kwarin guiwa, ya tabbatar da cewa Hisbah ba za ta sassauta ba wurin yaki da rashin da'a a unguwanni. 






SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "Kalli Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?