--
Hotunan budurwa mai shekaru 19 ta banka wa gidan tsohon saurayi wuta, ta kone sabuwar budurwarsa

Hotunan budurwa mai shekaru 19 ta banka wa gidan tsohon saurayi wuta, ta kone sabuwar budurwarsa


Hukumar 'yan sandan jihar Legas sun damki wata yarinya 'yar shekara 19, ranar 18 ga watan Nuwamba - An kama Jemila da kawarta wacce ta raka ta bisa zargin bankawa gidan tsohon saurayinta wuta, saboda zafin kishi 


Dakyar aka samu aka ceci sabuwar budurwarsa dake zaune a gidan, wacce dakyar asibiti suka ceto rayuwarta Hukumar 'yan sandan jihar Legas, ta kama wata yarinya 'yar shekara 19, mai suna Jemila Ibrahim da kawarta, Fatima Mohammed, mai shekaru 21 dake Monkey Village wurin Festac Area a Legas. 



Ana zarginta da banka wa gidan wani Mohammed Yusuf na Monkey Village a Legas, wacce budurwarsa Rabi, take zaune a gidan, a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba. 


Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Muyiwa Adejobi, ya ce Mohammed tsohon saurayin Jemila da ya ji labarin aukuwar lamarin, yayi gaggawar shiga gidan don ya ceto Rabi, sabuwar budurwarsa. 


Ya gaggauta kai ta Asibiti, inda aka samu aka ceci rayuwarta da kyar a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba, shafin Linda Ikeji ya wallafa. Mohammed ya zargi tsohuwar budurwarsa, Jemila Ibrahim da miyagun halaye kafin su rabu, tukunna ya hadu da Rabi, suka fara soyayya har kaddara ta afka mata.


Yanzu haka 'yan sanda sun kama Jemila Ibrahim da kawarta, Fatimo Mohammed ta Monkey Village, wacce ta raka Jemila wurin yin aika-aikar. Kwamishinan 'yan sanda na jihar Legas, CP Hakeem Odumosu, ya umarci a mayar da al'amarin bangaren binciken manyan laifuka na jihar, don a yi bincike da kyau. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Hotunan budurwa mai shekaru 19 ta banka wa gidan tsohon saurayi wuta, ta kone sabuwar budurwarsa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?