
Hotuna: Za a birne wani hamshaƙin attajiri tare da sunƙin daloli
Masu kudin Zimbabwe sun dauki alkawarin ɗaukan naiyin bikin binne Ginimbi - Iyalan Moana na neman kudin da zasu yi bikin jana'izarta daga masu fatan alheri
wata majiya ta kusa ta ruwaito. Dan kasuwar wanda ya yi rayuwa ta alfarma, shine ya bar wasiyar, a cewar jaridar Herald. Ginimbi ya rasu a wani hadarin mota daya afku ranar Lahadi a Harare tare da Mitchelle Amuli wadda aka fi sani da Moana.
Iyalan Moana suna neman kudin jana'izarta daga masu fatan alheri kamar yadda The Nation ta ruwaito. Iyalanta sun dage jana'izarta zuwa sati biyu don jiran sakamakon gwajin kwayar halitta na DNA da kuma tattara kudaden da ake bukuta don yi mata suturara da ta dace, kamar yadda rahoton Zim Morning ya shaida.
Masu kudi a Zimbabwe sun ɗauki alkawari ɗaukan nayin bikin binne Ginimbi. Wani mataimakin minista Tino Machakaire ya yi alkawarin siyawa Ginimbi akwatin gawa ƙirar Versace, dan majalisa Temba Mliswa ya bada tarin dabbobi don a yanka a wajen jana'izar, shi kuma wani dan siyasa, Acie Lumumba, ya yi alkawarin lita 1,000 na diesel, inji wata majiya ta kusa.
Duka Ginimbi da Moana suna kan hanyarsu ta dawowa daga wani taron shagali ne motar su tayi karo ta wata motar mai tahowa, kuma suka kauce daga titi tare da dukan wata bishiya kuma nan take ta kama da wuta.
SOURCE: Legit
0 Response to "Hotuna: Za a birne wani hamshaƙin attajiri tare da sunƙin daloli"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?