--
Hisbah ta yi bincike ɗaki-ɗaki don kama masu baɗala a Kano (Kalli Hotuna)

Hisbah ta yi bincike ɗaki-ɗaki don kama masu baɗala a Kano (Kalli Hotuna)


Hukumar Hisbah na ci gaba da kokarin tabbatar da shari'ar musulunci a arewa duk da rashin goyon bayan wasu yan Najeriya - Hukumar ta Hisbah ta gudanar da bincike ɗaki ɗaki a wurin shakatawa na Hills and Valley da ke birnin Kano ranar Juma'a don kama masu badala 


Ko a farkon watan nan, hukumar ta fasa kwaleben giya na sama da miliyan 300 a jihohin Katsina Kano da Kaduna Jami'an hukumar Hisbah a Jihar Kano ranar Juma'a sun gudanar da wani binciken kwakwaf a Hills and Valley, wani wajen yawon bude ido da shakatawa a Dawakin Kudu, da ke birnin Kano.





SaharaReporters ta ruwaito cewa an tilasta ma'aikatan wajen su zagaya da jami'an Hisbah duk gine ginen da ke wajen.




Lokacin binciken, jami'an Hisbah sun duba ko wane daki da sauran wurare don gano masu aikata 'badala'. Duk da wasu yan Najeriya ba sa goyon baya, hukumar Hisbah na ci gaba da kokarin kafa aƙidun musulunci a arewa. 


Hukumar ta kirkiri kafa dokokin musulunci a wasu jihohi, sun hana sun hana askin banza, ɗame wando, hana kaɗe kaɗe lokacin shagali da ƙwace Adaidaita da aka yi wa ado da hotunan da suka saɓa da tarbiyar musulunci. Hukumar ta kuma hana daukar mata biyu a baburin haya guda daya. 


A farkon watan nan, hukumar ta fasa kwalaben giya da suka haura naira miliyan 300 a jihohin Kano, Kaduna da Katsina. 


Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Hisbah ta yi bincike ɗaki-ɗaki don kama masu baɗala a Kano (Kalli Hotuna)"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?